'Yan Bindiga Sun Kawo Babban Cikas a Kokarin Ceto Daliban da Aka Sace a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Kawo Babban Cikas a Kokarin Ceto Daliban da Aka Sace a Kaduna

  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa sojoji sun inda ƴan bindigan da suka sace ɗalibai 287 a jihar Kaduna suke a cikin daji
  • Sai dai, ƴan bindigan sun koma yin amfani da ɗaliban wajen samun kariya yayin da dakarun sojojin suke dab da isa wajensu
  • Gwamnati dai ta sha alwashin ganin an ceto ɗaliban sun shaƙi iskar ƴanci bayan da ƴan bindigan suka kutsa har cikin makaranta suka yi awon gaba da su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Sojoji sun kusa cimma ƴan bindigan da suka sace ƴan makaranta 287 a Kuriga, ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a ranar Alhamis, cewar jaridar The Nation.

Sai dai an ce ƴan bindigar na amfani da mutanen wajen samun garkuwa yayin da jami’an tsaron ke isa zuwa gare su.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kaduna ta dauki hanyar ceto daliban da aka sace zuwa daji, bayanai sun fito

Sojoji sun kusa cimma 'yan bindiga a Kaduna
Gwamnati ta sha alwashin ceto ɗaliban Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Majiyar ta ce sojojin sun bi sahun ƴan bindigan ne biyo bayan umarnin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayar na a ceto yaran ko ta halin ƙaƙa da kuma cafke masu hannu a sace su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano inda ƴan bindigan suke

Majiyoyi sun shaida wa jaridar The Nation a Kaduna cewa sojojin da aka girke a dajin domin gudanar da bincike da aikin ceto, sun gano inda ƴan bindigan da ɗaliban suke.

An tattaro cewa tafiyar ƴan bindigan da ɗaliban a cikin dajin bata yin sauri, saboda yawan yaran da kuma ƙarancin shekarun su.

Majiyar ta bayyana cewa:

"Abin da muka tattaro shi ne ƴan bindigan ba su yi nisa da ɗaliban da aka sace ba saboda yaran da ke cikin waɗanda aka sace na rage musu sauri.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka kashe ƴan sanda da yawa a babban birnin jihar APC

"Yanzu, sojojin da suka bi su sun ga ƴan bindigan da waɗanda aka sace, amma aikin ceto su na da wahala a yanzu saboda ƴan bindigan na amfani da yaran a matsayin garkuwa."

An fara yunƙurin ceto ɗaliban Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ta fara yunƙutin ganin ta ceto ɗaliban da aka yi garkuwa da a jihar.

Majiyoyim sun yi nuni da cewa gwmanatin ta ɗauko wani sanannen mai shiga tsakani don tattaunawa da ƴan bindigan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel