“Za a Yi Bikin Kirsimeti Mai Matukar Hatsari”, Malamin Addini Ya Yi Hasashe Kan Disamba

“Za a Yi Bikin Kirsimeti Mai Matukar Hatsari”, Malamin Addini Ya Yi Hasashe Kan Disamba

  • Watan karshe na shekarar 2023 na gab da karewa, inda mutane da dama ke shirye-shiryen sabuwar shekara, 2024
  • Legit Hausa ta rahoto cewa malaman Najeriya da dama na ta hasashensu gabannin sabuwar shekara
  • Daya daga cikinsu shine Prophet Abel Boma, wanda ya yi hasashen Disamba mai muni a sakon da ya wallafa a dandalinsa na YouTube

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Port Harcourt, jihar Rivers - Prophet Abel Tamunominabo Boma ya bukaci jama'a da su dage da addu'a sosai a watan Disamban 2023.

A wani bidiyo da ya wallafa a dandalinsa na YouTube, Prophet Boma ya ce mutane masu yawan gaske za su mutu.

Malamin addini ya bukaci jama'a su dage da addu'a
“Za a Yi Bikin Kirsimeti Mai Matukar Hatsari”, Malamin Addini Ya Yi Hasashe Kan Disamba Hoto: Abel Tamunominabo Boma
Asali: UGC

"Ku dage da addu'a a wannan Disamba" - Prophet Boma

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin addini ya bayyana lokaci da yadda yake so ya mutu

Malamin addinin ya bayyana cewa "za a yi bikin kirsimeti mai matukar hatsari."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalamansa:

"A watan Disamba, don Allah kowa ya dage da addu'a sosai. A watan Disamba, ba za a ji ta da sauki ba. Za mu samu mutane masu yawan gaske. Ban san a ina za su kasance ba. Na gano wasu adadi na mutane, masu yawan gaske, ban san me ya faru ba, amma sun mutu.
"Mu yi addu'a, za a yi Kirsimeti mai hatsari."

Kalli bidiyon a kasa:

Makarkashiya za ta yi yawa a 2024

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa Boma ya ce za a yi "makirci" sosai a 2024. malamin addinin ya gargadi mutane da su yi taka tsantsan wajen mu'amalarsu da sauran mutane.

Ya kuma bayyana cewa wata cuta mai kama da korona za ta barke a cikin shekara mai zuwa don haka mutane su dunga rike katinsu na shaidar karbar rigakafin korona yayin da za su yi tafiya.

Kara karanta wannan

Yadda mutumin da ke aikin wanke bandaki a turai ya siya gida daga albashinsa, bidiyon ya yadu

A taya Shugaba Tinubu da addu'a, Boma

Haka kuma, malamin addinin ya bukaci yan Najeriya da su taya Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da addu'a.

Prophet Boma ya bukaci yan Najeriya da su yi wa shugaban kasar addu'a kan jinnu da mutuwar faran daya. Ya kuma ce ba zai zama nasara ga abokan hamayyar Shugaban kasa Tinubu ba don shugaban Najeriyan ya mutu a ofis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel