Ba Za Mu Iya Kawo Karshen Matsalar Ayyukan Yi Ba a Kasar”, Gwamnatin Tarayya

Ba Za Mu Iya Kawo Karshen Matsalar Ayyukan Yi Ba a Kasar”, Gwamnatin Tarayya

  • Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa ita kadai ba za ta iya dakile matsalar aikin yi ba a kasar
  • Gwamnatin ta ce a dukkan rukunai uku na gwamnatin ba za su iya magance matsalar ba
  • Ta bukaci dukkan ma su ruwa da tsaki a bangarori da dama da su kawo dauki don ganin an samo mafita

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba za ta iya kawo karshen rashin ayyukan yi ba a kasar.

Gwamnatin ta shawarci masu ruwa da tsaki a kasar da su tashi tsaye wurin ganin sun dakile matsalar da ke kawo cikas ga al’umma.

Gwamnatin Tarayya ta ce ba za ta iya kawo karshen rashin aikin yi ba a kasar
Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan rashin aikin yi a Najeriya. Hoto: Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Twitter

Me Gwamnatin Tarayya ta ce kan rashin aiki?

Daraktan ayyukan yi a ma’aikatar Ayyuka da Kwadago, Dakta John Nyamali shi ya bayyana haka yayin wani taro na samar da aikin yi a jihar Ogun, Tribune ta tattaro.

Kara karanta wannan

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Dira Jihar Arewa, Ya Aike da Kakkausan Saƙo Ga Yan Ta'adda, Ya Ba Su Zaɓi 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nyamali ya ce gwamnatoci na bukatar masu ruwa da tsaki wurin tsare-tsare da gudanarwa da kuma kula da ayyuka.

Ya ce a tsarin samar da ayyukan yi a kasa, an bayyana yadda jihohi da kananan hukumomi za su taka rawa don samar da ayyukan yi.

Ya ce babu daya daga cikin rukunan gwamnati da za ta iya kawo karshen matsalar a kasar.

A kwanakin baya, Shugaba Tinubu ya yi alkawarin cire yan Najeriya miliyan 133 daga kangin talauci wanda ya hada da samar da ayyukan yi ga matasa.

Wasu tsare-tsare Gwamnatin Tarayya ta yi na samar da aikin yi?

Dakta Betta Edu, ministar Jin Kai da Walwala ita ta bayyana haka inda ta ce Tinubu ya himmatu wurin samar da ayyukan yi da za su cire mutane a kangin talauci.

Dalilin haka ne ma gwamnatin ta dawo da shirin ‘Tradermoni’ da ake bai wa kananan ‘yan kasuwa don kara musu jari.

Kara karanta wannan

Damu ake: Birtaniya ta ce za ta tura sojojinta su taya Isra'ila yakar dakarun Hamas

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari shi ne ya kawo tsarin inda ya ke bai wa ‘yan kasuwan Naira dubu 10, Headlines.ng ta tattaro.

Amma a wannan karon, Tinubu ya inganta shirin inda zai rika ba da Naira dubu 50 a matsayin lamuni ga kananan ‘yan kasuwa a kasar.

Tinubu ya dakatar da shirin N-Power saboda matsaloli

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da shirin matasa na N-Power saboda wasu matsaloli da ke tattare cikin shirin.

Ministar Jin Kai da Walwala, Dakta Betta Edu ita ta bayyana haka yayin hira da ‘yan jaridu a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel