“Daga Yanzu Ba N8k”: Gwamnatin Tarayya Za Ta Turawa Iyalai Miliyan 15 N75,000 Na Watanni 3

“Daga Yanzu Ba N8k”: Gwamnatin Tarayya Za Ta Turawa Iyalai Miliyan 15 N75,000 Na Watanni 3

  • Gwamnatin Najeriya ta ce za ta bai wa iyalai masu karamin karfi miliyan 15 kudi N75,000 cikin watanni uku
  • Ma'aikatar Jin Kai da Yaki Da Talauci ta ce za a raba kudaden ne a kashi uku tsakanin Oktoba da Disamban 2023
  • Ministar jin kai da rage radadin talauci, Betta Edu, ta ce ma’aikatarta ta yi wa yan Najeriya tanadi na musamman

Ministar Jin Kai da Yaki Da Talauci, Betta Edu, ta bayyana cewa gwamnatin Najeriya za ta tallafawa masu karamin karfi miliyan 15 karkashin shirin raba kudi.

Ministar ta bayyana hakan ne a ranar Talata, 3 ga watan Oktoba, yayin ziyarar da ta kai wa ministan labarai, Mohammed Idris.

Tinubu da ministar jin kai
“Daga Yanzu Ba N8k”: Gwamnatin Tarayya Za Ta Turawa Iyalai Miliyan 15 N75,000 Na Watanni 3 Hoto: Bloomberg / Contributor
Asali: Getty Images

Gwamnatin tarayya ta tanadi shirye-shiryen tallafawa al'umma

Kakakin ma'aikatar labarai, Rhoda Ishaku Iliya, ta bayyana a ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba, cewa ma'aikatar ta tanadi shirye-shirye iri-iri don saukaka wahalhalun da yan Najeriya ke ciki.

Kara karanta wannan

Kungiyar NLC Ta Fadi Yawan Mafi Karancin Albashi Da Za Su Tattauna Da Gwamnati, Ta Yi Wa Ma'aikata Albishir

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta bayyana cewa Edu za ta gudanar da shirye-shirye daban daban domin fitar da yan Najeriya daga talauci.

Kamar yadda Edu ta bayyana, gwamnatin Najeriya za ta samar da matsuguni, abinci mai gina jiki, da sauran matakan kare rayuwar yan Najeriya da ibtila'i ya afka masu.

Ta ce a karkashin shirin kawar da talauci, ma'aikatarta za ta kaddamar da shirye-shirye da dama domin fitar da yan Najeriya daga cikin talauci.

Za a raba kudaden sau uku

Jaridar Guardian ta rahoto cewa Edu ta bayyana cewa shirye-shiryen sun hada da yakar yunwa, tallafi, bayar da tallafi ga kungiyoyin masu karamin karfe, da kuma shirin sabonta muhalli.

"Ta bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta tallafawa iyalai miliyan 15 karkashin shirin CCT inda za a biya duk wanda ya amfana N75,000 a biya uku," inji Illiya.

Kara karanta wannan

Babu Wata Yarjejeniya Da Emefiele Kan Dawo da ‘Biliyan 50’, Gwamnatin Tinubu

“Dr. Edu ta kuma bayyana cewa mutane miliyan 1.5 za su ci gajiyar shirin GEEP wanda zai fara a watan Oktoban 2023. Duk wanda ya ci gajiyar shirin zai karbi N50,000 a karkashin shirin bada lamuni na Matan Kasuwar GEEP, yan kasuwa, da shirin ba manoma bashi. Za a biya kudaden ne a matakai 3 da mutane 500,000 a kowane mataki," inji sanarwar.

Shugaba Tinubu ya karawa ma’aikata alawus a yunkurin Hana ‘yan kwadago yajin aiki

A wani labarin, mun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na bakin kokarinsa na ganin an daina maganar shiga yajin-aikin da sai baba-ta-gani a kasar nan.

Sanarwa ta fito daga fadar shugaban kasar cewa an amince ayi wa ma’aikatan gwamnatin tarayya karin N10, 000 kan alawus din da za a raba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel