Tallafi Ya Dawo bayan Tinubu Ya Biya Naira Biliyan 169 A Agusta Don Tsayar Da Farashin Lita a N620

Tallafi Ya Dawo bayan Tinubu Ya Biya Naira Biliyan 169 A Agusta Don Tsayar Da Farashin Lita a N620

  • Alamu na nuna cewa Gamnatin Najeriya ta dawo da tallafi yayin da ta biya makudan kudade a watan Agusta
  • Gwamnatin ta biya Naira biliyan 169.5 na tallafi don tabbatar da farashin litar mai ya tsaya kan Naira 620
  • Rahotanni sun tabbatar cewa yanayin farashin litar mai a yanzu zai fi dorewa ganin yadda gangan mai ta kai Dala 95

FCT, Abuja – Rahoton da ke samun mu na cewa Gwamnatin Tarayya ta biya Naira biliyan 169.4 na tallafin mai a watan Agusta.

Gwamnatin ta biya kudin tallafin ne don tabbatar da cewa farashin litar mai ta tsaya a kan Naira 620 ba tare da ta yi sama ba.

Tinubu ya biya Naira tiriliyan 169 a watan Agusta
Tallafi Ya Dawo Yayin Da Tinubu Ya Biya Naira Tiriliyan 169 A Agusta. Hoto: Bola Tinubu, NNPC.
Asali: Facebook

Meye dalilin biyan kudin tallafin da Tinubu ya yi?

Rahotan Daily Trust ya tabbatar cewa yanayin farashin litar mai a yanzu zai fi dorewa ganin yadda gangan mai ta kai Dala 95 a kasuwannin duniya.

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Girka Abinci Iri-Iri, Ta Ce Kudinsu Miliyan 3.2 Yayin da Ta Baje Kolinsu a Bidiyo

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit ta tattaro cewa Hukumar Rarraba Kudade (FAAC) ta ce hukumar samar da iskar gas ta biya NNPC Dala miliyan 220 don biyan kudin tallafi tare da rike Dala miliyan 55.

FAAC ta ce tallafi ya dawo kasar yayin da kamfanin NNPC ya biya da kudaden iskar gas.

Tsohowar gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta fi ko wace biyan kudin tallafi mafi yawa a kasar.

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu mutane a kan wannan lamari.

Wani dan kabu-kabu, Muhammad Abubakar ya ce wannan ai shirme ne idan dai ba rage farashin litar zai yi ba.

Ya ce:

"Lokacin da na samu labarin, na bincika sai na ga ba kamar yadda na ke tsammani ba ne, aikin banza ne ai tunda farashin lita ba zai ragu ba."

Kara karanta wannan

Elon Musk Ya Bayyana Shirin Fara Biyan Kudi Duk Wata Ga Masu Amfani Da Twitter, Ya Bayyana Dalili

Wani mai matsa mai a gidajen mai da ke Gombe da bai so a ambaci sunansa ba ya ce:

"Haka ne abin da ake fada amma mu so muke farashin ta sauko saboda ciniki ya ja baya, mu na shan wahala."

Yayin da Ali Achaba ya ce In shaa Allah farashin litar za ta sauko a hankali mu na fatan haka.

Nawa ake biyan kudaden tallafin kafin Tinubu?

Kamfanonin man fetur da kuma iskar gas sun bayyana cewa yawan kudaden tallafi da ake biya daga 2015 zuwa 2020 ya kai Naira tiriliyan 1.99.

Yayin da kamfanin NNPC ya ce biyan kudin tallafi a shekarar 2021 Naira tiriliyan 1.57 inda a farkon 2022 ya sauko zuwa Naira tiriliyan 1.27.

Gwamnatin Najeriya ta ware Naira tiriliyan 3 don biyan kudaden tallafi daga watan Yunin 2022 zuwa Yuni na 2023.

Jimilar lissafin ta tabbatar da cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kashe Naira tiriliyan 7.83 a kan biyan kudaden tallafi kadai.

Kara karanta wannan

Dillalan Iskar Gas Sun Bayyana Yadda Farashin Zai Kasance Zuwa Watan Disamba, Sun Fadi Dalili

Tinubu ya bai wa 'yan Najeriya hakuri kan cire tallafi

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya roki 'yan Najeriya su kara hakuri kan cire tallafi da aka yi.

Tinubu ya ce nan gaba kadan 'yan kasar za su dara kuma za su manta da maganar cire tallafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel