Zababbun Sanatocin APC 2 Su na Rububi a Kan Kuri’un ‘Yan PDP a Majalisar Dattawa

Zababbun Sanatocin APC 2 Su na Rububi a Kan Kuri’un ‘Yan PDP a Majalisar Dattawa

  • Bola Tinubu yana goyon bayan Sanata Godswill Akpabio da Sanata Barau Jibrin a zaben ‘Yan majalisa
  • Babu tabbaci a kan wadanda za su zama shugabannin majalisa, Abdulaziz Yari ya huro wuta da gaske
  • Tsohon Gwamnan Zamfara ya samu wasu manyan Sanatoci da ke mara masa baya wajen ‘yan PDP

Abuja - A kokarin ganin sun yi nasara a zaben majalisa, Abdulaziz Yari (Zamfara) da Godswill Akpabio (Akwa Ibom) sun komawa jam’iyyar adawa.

Rahoton da aka samu daga Daily Trust ya nuna Godswill Akpabio da Abdulaziz Yari su na kokarin ganin yadda za su samu samu kuri’un Sanatocin PDP.

‘Yan siyasar biyu su na cikin zababbun ‘yan majalisar dattawan da za a rantsar a jam’iyyar APC.

Da alama tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari bai hakura da takararsa ba, yana cikin wadanda suka cije duk da bai cikin manyan Sanatoci.

Kara karanta wannan

APC Ta Sake Korar Wani Sanata Bayan Gano Cin Amanar da Ya yi wa Jam’iyya a Zabe

Ana harin sababbin shiga

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa Abdulaziz Yari ya na bakin kokarinsa domin samun goyon bayan zababbun Sanatocin da suka lashe zabe a PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Baya ga haka, akwai Sanatocin jam’iyyar APC mai rinjaye da ke tare da tsohon gwamnan.

Zababbun Sanatoci
Sanatoci bayan zaman Majalisa Hoto : @NgrSenate
Asali: Facebook

Wanda ya iya allonsa

Wasu gungun Sanatoci da ke da tsofaffin Gwamnoni hudu daga jihohin Arewacin Najeriya su na goyon bayan Yari, su na so ya zama shugaban majalisa.

Rahoton ya ce wadannan Sanatoci daga Arewa maso yamma da Arewa maso gabas su na faman lallabar sababbin shiga majalisa domin samun kuri’unsu.

“’Yan PDP da ke APC wadanda tsofaffin Gwamnoni ne sun jawo wani tsohon shugaban majalisar dattawa domin a maimaita irin abin da aka yi a 2015.
Su na tara dukiya domin su cin ma manufarsu. Burinsu shi ne samun Sanatoci 60 daga dukkanin jam’iyyu su goyi bayan wannan aiki da suka dauko.”

Kara karanta wannan

‘Dan Majalisar Kano da Ake Zargi da Kisan Kai Ya Fito Takarar Shugaban Majalisa

- Majiya

Godswill Akpabio

Yayin da ‘Yan kudu maso gabas su ke kokarin ganin sun samu wannan kujera, ‘yan siyasar yankin da na Neja Delta ba su gamsu da zabin Sanata Akpabio ba.

A gefe guda, Yari yana ganin daga Arewa ya kamata a samu wanda zai gaji Ahmad Lawan. Kafin shigansa APC a 2018, Akpabio ne shugaban marasa rinjaye.

Hadin gwiwa a majalisa

A wani labari na dabam, an ji ‘yan APC da PDP sun hadu da jam’iyyun LP, NNPP da kuma APGA, sun kafa wata kungiyar hadaka a majalisar wakilai na kasa.

Kungiyar ta na da wakilci daga jam’iyyun SDP, ADC da YPP, ba a gama gane manufarsu ba tukun duk da sun nuna ba za su hana APC yin shugabanci ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel