Dan Takarar APC Bomai Ya Lashe Zaben Sanatan Yobe Ta Kudu da Aka Kammala Yau

Dan Takarar APC Bomai Ya Lashe Zaben Sanatan Yobe Ta Kudu da Aka Kammala Yau

  • Rahoton da muke samu daga jihar Yobe ya bayyana cewa, dan takarar sanatan APC ya lashe zabe a mazabar Yobe ta Kudu
  • Ibrahim Bomai ne hukumar ta sanar ya lashe zabe, bayan cikata kada kuri’un da aka yi a yau Asabar 15 ga watan Afrilu
  • Ana ci gaba da sanar da sakamakon cikon zaben da ake yi a Najeriya bayan da aka dakatar dashi a watan jiya na Maris

Jihar Yobe - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a jihar Yobe ta ayyana Ibrahim Bomai a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan mazabar Yobe ta Kudu a majalisar dattawa, Channels Tv ta ruwaito.

A cewar sakamakon zaben na yau Asabar 15 ga watan Afrilu, baturen zabe, Abatcha Melemi ya bayyana cewa, Bomai na APC ya samu kuri'u 69,596, inda ya lallasa abokin hamayyarsa na PDP, Halilu Mazagane da ya samu kuri'u 68,885.

Kara karanta wannan

Zaben yau Asabar: Mata sun tona asirin APC a jihar Arewa, sun fadi yadda ake ba su kudi

APC ta lashe kujerar sanata a Yobe
Jihar Yobe da ke Arewa maso Gabas | Hoto: thenationoneng.net
Asali: Facebook

Wannan na nuna cewa, Bomai ne zai tafi majalisar dattawa ta 10 da ake shirin kafawa nan ba da jimawa ba a watan Yuni.

Yadda zaben Yobe ya kaya a baya

A tun farko, hukumar zabe ta dakata da tattara sakamakon zaben yankin tare da ayyana shi 'inconclusive' saboda wasu dalilai na aringizon kuri'u a rumfunan zaben Manawachi a karamar hukumar Fika.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga baya, an sanar da cikon zaben a yau Asabar don karasa zaben daga inda aka tsaya a watan Faburairun da ya gabata.

Da yake sanar da manema labarai sakamakon zaben, baturen zaben ya ce abin da ya fada gaskiya ne kuma shi ne adalci.

Kudi, taliya da atamfa aka bamu mu zabi APC, inji mata a Kebbi

A wani labarin, kunji yadda wasu mata suka fito suka shaida yadda aka yi musu sayen baki a wani yankin jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Waiwaye: Yawan Kuri'un Da APC, PDP Ke Da Shi Kafin INEC Ta Ayyana Zabukan Adamawa, Kebbi a Matsayin Wadanda Basu Kammala Ba

A cewar matan, jam'iyyar tsintsiya ce ta tara su tare da basu kudi N3000, atamfa da taliya domin kawai su ba da kuri'unsu a cikon zaben gwamnan jihar.

A tun farko an dakata da tattara sakamakon zaben jihar tare da bayyana za a sake yin zaben a wasu yankunan da aka samu tsaiko a ranar 18 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel