Yan Bindiga Sun Kaiwa Dan Takaran Gwamnan Jihar Ebonyi Hari An Kashe Direbansa

Yan Bindiga Sun Kaiwa Dan Takaran Gwamnan Jihar Ebonyi Hari An Kashe Direbansa

  • Yankin kudu maso gabashin Najeriya ya yi kaurin suna da kaiwa yan takarar siyasa harin kisa
  • An kaiwa Gwamnan Anambra hari, an kaiwa Sanata Uba hari, yanzu kuma dan takarar gwamna
  • Hadimin dan takaran ya ce wannan shine karo na biyu da za'a kaiwa maigidansa hari

Ebonyi - Dan takarar kujerar gwamnan jihar Ebonyi karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, Farfesa Bernard Odo, ya tsallake rijiya da baya bayan mumunan harin da aka kai masa.

Direbansa dai bai yi sa'a ba, sun kashe shi har lahira yayinda sauran dogaransa suka samu rauni munana, rahoton SR.

Enonyi
Yan Bindiga Sun Kaiwa Dan Takaran Gwamnan Jihar Ebonyi Hari An Kashe Direbansa Hoto: @saharareporters
Asali: Twitter

Rahotanni sun nuna cewa Farfesa Odo, wanda tsohon sakataren gwamnan jihar ne lokacin wa'adin farko na gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, na hanyar dawowa daga kamfe a Agba.

Yana hanya ne wasu yan bindiga suka bude masa wuta a unguwar Rest Haius, titin Enugu/Abakaliki.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan Bindiga Sun Bude Wa Ayarin Motoccin Dan Takarar Gwamna Wuta, Sun Bindige Direbansa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tattaro cewa yan bindigan sun fito daga motarsu kirar Toyota Sienna suka bude masa wuta kuma sun ragargaza motar gaba daya, riwayar Punch.

Tsohon hadiminsa, Mr Godwin Chinonso, ya bayyana cewa wannan shine karo na biyu da za'a kaiwa maigidansa hari.

Karon farko an kai masa hari a karamar hukumar Izzi inda ya tafi kamfe.

Yace:

"Na tafi dakin ajiye gawawwaki na asibiti inda aka kai gawar direbansa. Sauran dogaransa na jinya yanzu haka a asibiti dake Abakaliki."
"Yan bindigan sun kona motarsa. Wannan abu ya auku ne misalin karfe 9 na daren Alhamis."

Duk yunkurin ji ta bakin Kakakin yan sandan jihar, SP Chris Anyanwu, ya ci tura.

Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Alkalin Kotu Cikin Kotu Yana Yanke Hukunci

A wani labarin mai kama da wannan, wasu yan bindiga sun bindige Alkali kuma shugaban kotun kostomaren Ejemekwuru, Nnaemeka Ugboma, har lahira ranar Alhamis, 3 ga Febrairu, 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin APC Zasu Shiga Ganawar Sirri Da Buhari Kan Lamarin Naira Da Tsadar Mai

Wannan abu ya auku ne a karamar hukumar Oguta ta jihar Imo.

Leadership ta ruwaito wani mai idon shaida da cewa yan bindigan sun dira harabar kotun kan babura kuma suke garzaya kai tsaye cikin kotun ana tsaka da zama.

Ya ce nan take suka fito da alkalin waje kuma suka bindigeshi suka kama gabansu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel