Don 'Ya'yansa 31 Yake Yi: Tsohon Hadimin Atiku Ya Tona Asiri, Ya Fadi Dalilin Da Yasa Atiku Ke Son Gaje Buhari

Don 'Ya'yansa 31 Yake Yi: Tsohon Hadimin Atiku Ya Tona Asiri, Ya Fadi Dalilin Da Yasa Atiku Ke Son Gaje Buhari

  • Michael Achimugu ya fito ya sake yi wa dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar terere gabannin babban zaben 2023
  • Tsohon hadimin dan takarar na PDP ya ce Atiku na da kudirin ganin yaransa sun zamo attajirai kamar shi bayan ya mutu don haka yake son gaje Buhari
  • Achimugu idan har yan Najeriya na son magana ta gaskiya toh lallai shigar Atiku Aso Rock babban kalubale ne ga kasar

Michael Achimugu ya gargadi yan Najeriya a kan zabar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar a zabe mai zuwa, cewa shi din ba mutumin kirki bane.

Achimugu wanda ya kasance tsohon hadimin Atiku ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a wani shiri na TVC a ranar Laraba, 25 ga watan Janairu, yana mai cewa shugabancin Atiku zai zamo annoba ga yan Najeriya.

Kara karanta wannan

'Kana Bukatar Taimako', Martanin Fadar Shugaban Kasa Ga Kalaman Tanko Yakasai Kan Tinubu

Atiku da jiga-jigan APC
Don 'Ya'yansa 31 yake yi: Tsohon Hadimin Atiku Ya Tona Asiri, Ya Fadi Dalilin Da Yasa Atiku Ke Son Gaje Buhari Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Atiku na son zama shugaban kasa don ya azurta yaransa 31, Achimugu

Har ila yau, Achimugu ya ce tsohon ubangidan nasa na son zama shugaban kasar Najeriya ne saboda yara 31 da ya haifa, cewa so yake yi su zamo attajirai tamkar shi idan baya doron kasa, rahoton Sahara Reporters.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi ikirarin cewa kamar yadda suke yi a jihar Adamawa wajen fafutukar samun manyan mukamai, haka suke niyan yi idan har ya samu damar shiga fara shugaban kasa.

Ya ce:

"Atiku ba yaro bane. A duk sanda ya mutu, yana so yaransa su zamo attajirai kuma masu iko kamar shi. Wasu lokutan akwai misalai da dama a Najeriya, haka tara wannan arziki na 'ya'ya, jikoki da tattaba kunne.
"Don haka kamar yadda suke yi a jihar Adamawa, a kodayaushe suna fafutukar samun manyan mukamai masu tsoka, shine abun da suke niyan yi idan ya samu shiga Aso Rock.

Kara karanta wannan

2023: Babban Jigon PDP Ya Faɗi Sunayen Jihohin Da Atiku Zai Sha Kaye a Zabe Da Dalilai

"Amma kamar yadda na yi wa yan Najeriya bayani, ba kimiyyar roka bane, wannan mutumin (Atiku) yana da yara 31 da ya haifa a cikinsa, 30 daga cikinsu balagaggu ne.
"Dukkanin wadannan balagaggun na son zama biloniya. Zai tatse albarkatun kasar nan sosai ko kuna so ko ba ku so, kawai ku fahimci gaskiyar magana kuma wannan ba abu ne da za mu iya daukarsa a wannan lokaci da muke ciki a yauwar Najeriya."

Har ila yau, Achimugu ya ce ya fallasa badakalar tsohon ubangidan nasa ne domin hana yan Najeriya yin babban kuskure ta hanyar zabansa, rahoton Punch.

Ku zabi mijina don Yarbawa su samar da matar shugaban kasa - Titi Atiku

A wani labarin, matar Atiku Abubakar, Titi ta bayyana kudirinta na son zama matar shugaban kasa Bayarbiya ta farko.

A cewarta tun bayan dawowar mulkin damokradiyya, yankin kudu maso yamma bai samar da matar shugaban kasa ba don haka take son rusa wannan tarihi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel