Kuyi Hakuri Amma Ba Zamu Kara Wa'adin Daina Amfani Da Tsaffin Naira Ba, Emefiele

Kuyi Hakuri Amma Ba Zamu Kara Wa'adin Daina Amfani Da Tsaffin Naira Ba, Emefiele

  • Ana saura kwanaki 7 kacal karewar wa'adin tsaffin Naira, gwamnan CBN ya fito yayi magana
  • Godwin Emefiele ya ce gaskiyar magana itace ba za'a dage wa'adin 31 ga Junairu da aka sanya ba
  • Emefiele yace wannan shine ra'ayin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a bayanansa

Abuja - Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Mr Godwin Emefiele, ya bayyana cewa yan Najeriya suyi hakuri amma ba zai sauya ranar daina amfani da tsaffin takardun kudin Naira ba.

Emefiele ya bayyana hakan ne ranar Talata, 24 ga Junariu, 2023 bayan zaman MPC a birnin tarayya Abuja.

Ya bayyana cewa shi dai har yanzu bai ga dalilin da zai sa a kara wa'adin ba saboda an baiwa jama'a kwanaki 100 su mayar da kudadensu banki.

Ya ce ko shugaba Muhammadu Buhari ya fadi hakan sau biyu cewa duk mai kudin halal, kwanaki 100 sun isa ya mayar da kudadensa banki.

Kara karanta wannan

Duk da umurnin Buhari, Bayan Umurnin Buhari, Har Yanzu Ko N200 Ba'a Samu a Bankuna

Tsohon
Kuyi Hakuri Amma Ba Zamu Kara Wa'adin Daina Amfani Da Tsaffin Naira Ba, Emefiele
Asali: Getty Images

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A rahoton ChannelsTv, Emefiele ya bayyana cewa:

"Gaskiya ayi hakuri bani da wani labari mai dadi ga wadanda ke son a dage ranar daina amfani da tsaffin kudi. Ina mai bada hakuri."
"Dalili kuwa shine kamar yadda shugaban kasa ya fadi akalla sau biyu cewa kwanaki 100 ya isa ga kowa ya mayar da kudinsa banki."
"Kuma mun dau duk matakan ganin cewa bankuna na bude don karban tsaffin kudin mutane. Kwanaki 100 sun isar gaskiya."
"Mun bukaci bankuna su kara lokacin aiki kuma har ranar Asabar."
"Babu wani dalilin da zai sa a dage sbaoda mutane sun ki mayar da tsaffin kudinsu baki."

Kalli bidiyon jawabinsa:

Saura kwanaki bakwai wa;adin 31 ga Junairu

Kawo yau 24 ga watan Juaniru, 2023, yan Najeriya da dama sun bayyana cewa har yanzu bankuna ba bada tsaffin kudade maimakon sabbi.

Kara karanta wannan

Na Kadu Da Jin Yadda Gwamnonin APC Ke Caccakar Buhari Kan Sauya Kudi, Kwankwaso

Legit ta zanna da wasu daidaikun yan Najeriya inda suka bayyana ra'ayoyinsu game da lamarin daina amfani da tsaffin kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel