Kotun Daukaka Kara Ta Sallami Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, Ta Kallubalanci Hukuncin Babban Kotu

Kotun Daukaka Kara Ta Sallami Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, Ta Kallubalanci Hukuncin Babban Kotu

  • Kotun daukaka kara a Abuja ta wanke tare da sallamar shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu da ya dade a tsare
  • Tawagar alkalai uku a kotun na daukaka kara sun yi watsi da zargin ta'addanci da cin amanar kasa da FG ta yi wa Kanu
  • Wasu lauyoyi masu kare hakkin bil adama sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta saki shugaban na IPOB ba tare da bata lokaci ba

FCT Abuja - Kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta sallami shugaban haramtaciyyar kungiyar Indigenous People of Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu, Channels Television ta rahoto.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta gurfanar da Kanu ne a babban kotun tarayya da ke Abuja kan tuhume-tuhume 15 masu alaka da cin amanar kasa da ta'addanci da ta ke zargin ya aikata yayin fafutikan neman ballewa daga Najeriya.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda masoya Nnamdi Kanu ke murna a cikin kotu bayan wanke shugaban IPOB

Kanu Nnamdi
Kotun Daukaka Kara Ta Sallami Nnamdi Kanu, Ta Kallubalanci Babban Kotu. Hoto: @ChannelsTV.
Asali: Twitter

Alkalai uku a kotun daukaka kara sun ce babban kotun na tarayya ba ta da hurumin yi masa shari'a duba da cewa yadda aka sace shi aka dawo da shi Najeriya ya saba wa dokokin OAU.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kotun ta ce tuhume-tuhume 15 da aka yi wa Kanu bai bayyana wuri, rana, lokaci da yanayin laifukan da ya aikata ba kafin a dawo da shi Najeriya ba bisa ka'ida ba, tare da saba dokokin kasa da kasa.

Kotun ta kara da cewa gwamnatin tarayya ta gaza bayyana inda aka kama Nnamdi Kanu duk da irin manyan zargin da ta ke masa.

Deji Adeyanju da Sowore sun yi kira ga gwamnati ta saki Kanu nan take

A bangarensu, masu rajjin kare hakkin bil adama, Deji Adeyanju da Omoyele Sowore sun bukaci gwamnatin tarayya ta saki Kanu nan take bayan hukuncin kotun daukaka karar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Wanke Nnamdi Kanu, Ta Umurci Gwamnati Ta Sake Shi

Yayin da Sowore, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Action Congress ya rubuta a twitter cewa #FreeNnamdiKanu

Adeyanju, a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce dole a saki shugaban na IPOB nan take.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel