Sakamakon Binciken da Muka Gudanar Kan Tukur Mamu Yana Da Daure Kai, DSS

Sakamakon Binciken da Muka Gudanar Kan Tukur Mamu Yana Da Daure Kai, DSS

  • Hukumar tsaron farin kaya ta mayar da martani ga shahararren malamin Musulunci, Ahmad Gumi kan kamun hadiminsa da tayi
  • DSS ta ce sakamakon binciken da tayi a kan Tukur Mamu akwai ban mamaki don haka ba za ta bari kalaman mutane su shagaltar da ita ba
  • Ta kuma ce ba za ta sake yin martani kan lamarin ba yayin da ta umurci jama'a da su guji yin kalaman ganganci sannan su jira hukuncin kotu

Abuja - Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta ce sakamakon binciken da ta gudanar kan Tukur Mamu akwai ban mamaki sosai, Daily Trust ta rahoto.

Da take martani ga furucin da shahararren malamin Musulunci mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi yayi, hukumar ta ce ba za ta bari ta shagaltu ba.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Maka ASUU A Kotu Bayan Sun Gaza Cimma Matsaya A Tattaunawarsu

Tukur Mamu
Sakamakon Binciken da Muka Gudanar a Gidan Tukur Mamu Yana Da Daure Kai, DSS Hoto: @pmnewsnigeria
Asali: Twitter

Gumi ya zargi DSS da aikata ta’addanci, yana mai kalubalantar rundunar yan sandan ta farin kaya da ta saki Mamu, wanda ya kasance hadiminsa ko kuma ta gaggauta gurfanar da shi a kotu.

Gumi ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ku kai shi kotu don fuskantar shari’a. Tsare shi duk da kasancewarsa magidanci mai iyali kawai don razanar da shi ne. Wannan razanarwar ma ta’addanci ne. Kama mutane saboda zalunci shima ta’addanci ne; kamar yadda yan ta’addan suke yi ta hanyar zuwa gidan mutum su yi garkuwa da shi.”

Da yake martani a cikin wata sanarwa da ya saki a daren ranar Lahadi, 11 ga watan Satumba, kakakin hukumar, Peter Afunanya, ya ce a kyale DSS ta aiwatar da aikinta.

Sai dai kuma, Afunanya, ya ce DSS ba za ta sake yin martani kan kamun Mamu ba tunda kotu za ta yanke hukunci kan lamarin.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: Buhari Baya Kaunar Najeriya Yadda Nake Sonta

PM News ta nakalto inda yake cewa:

“Hukumar tsaron farin kaya (DSS), ta bibiya tare da nazari a tsanaki kan yadda wasu sassa na jama’a ke cece-kuce game da lamarin kamu da binciken Tukur Mamu.
“Hukumar na burin cewa ba za ta shagala da wasu bayanai da ke yawo a kafofin watsa labarai ba.
“Maimakon haka, tana neman a kyaleta ta mayar da hankali kan binciken da ke gudana, wanda sakamakonsa ke cike da abubuwan ban mamaki.
“A halin da ake ciki, hukumar ba za ta ci gaba da yin martani kan lamarin ba tunda kotu za ta yanke hukuncita kan haka.
“Saboda haka, ana umurtan jama’a da su janye daga yin kalaman ganganci sannan su jira zaman kotu.”

Sheikh Ahmad Gumi Yayi Maganarsa Ta Farko Kan Kama Tukur Mamu

A baya mun ji cewa shahrarren Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi kira ga Hukumar tsarin farin kaya, DSS, ta gaggauta sakin Tukur Mamu ko ta kai shi kotu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Iyalan Tukur Mamu Wanke Shi Daga Zargi, Sun Bayyana Wanda Ke Da Kayan Sojojin Da DSS Ta Gano A Gidansa

Gumi ya bayyanawa gwamnati cewa dokar kasa bata amince a rike mutum sama da kwana guda ba'a kai shi kotu ba.

A zaman karatun littafin Muktasarul-Khalil da Malamin ke yi mako-mako a Masallacin Sultan Bello dake Kaduna, Gumi yace wannan jarabawa ce ga Tukur Mamu kuma Allah ya sa yaci jarabawar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel