Da Duminsa: Gini Ya Rikito, Ya Danne Ma'aikata Masu Yawa a Abuja

Da Duminsa: Gini Ya Rikito, Ya Danne Ma'aikata Masu Yawa a Abuja

  • Wani bene mai hawa biyu da ake kan ginawa a yankin Kubwa ya rikito inda ya danne ma'aikatan dake ginin
  • Tuni dai hukumar taimakon gaggawa ta NEMA ta ziyarci wurin inda take ta zakulo mutane tare da ceto su
  • Sai dai har yanzu ba a tabbatar da yawan wadanda ginin ya danne ba amma na fara mika jama'ar da suka jigata asibiti

Kubwa, Abuja - Wani bene mai hawa biyu da ake tsaka da gininsa ya rikito a yankin Kubwa dake Abuja, lamarin da ya kawo dannewar ma'aikata a cikin ginin.

Jami'an Hukumar Kula da Taimakon Gaggawa, NEMA, suna kokarin ceto jama'ar da ginin ya murkushe a yayin da Daily Trust ta ziyarci wurin.

Building Collapse
Da Duminsa: Gini Ya Rikito, Ya Danne Ma'aikata Masu Yawa a Abuja. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Bidiyoyin Shagalin Dinan Kyakkyawar Diyar Sanata Sahabi

Har yanzu babu tabbacin yawan wadanda lamarin ya shafa, amma wani mazaunin yankin yace wadanda suka samu rauni an kwashesu tare da mika su asibiti.

Hafeez Olayinka, daya daga cikin wadanda aka ceto bayan faduwar ginin a Abuja a safiyar Juma'a, yace ya kwashe sa'o'i a karkashin ginin.

Olayinka wanda ya koma wurin da lamarin ya faru bayan an bashi taimako daga asibiti, ya sanar da manema labarai cewa ya isa wurin ginin tun ranar Juma'a.

"Ni tare da wasu muna cikin ginin tun daren Alhamis. Tun ranar Litinin na zo wurin nan domin yin wasu gyara a ginin.
"Wurin karfe 11:30 na daren Alhamis, mun gane cewa ginin faduwa yake kokarin yi sai muka nemi tserewa amma ba mu samu dama ba. Mu biyar aka ceto da safiyar nan kuma aka mika mu asibiti," yace.

A zantawafr da Legit.ng tayi da Hadiza Gambo, mazauniyar Kubwa amma ma'aikaciya a UBEC, ta bayyana cewa bata da nisa da inda ginin ya rushe kuma tun dare lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Rikici: Basarake ya mance da batun rawani ya tsere yayin da 'yan daba suka farmaki fadarsa

"Mu kan wuce inda ake ginin benen, katon kanti ake ginawa. Cikin daren Alhamis ya rushe kuma ya murkushe wasu jama'a da har yanzu ba za a ce ga yawansu ba. Sai dai ko da safen nan ana ta kokarin ganin an ceto su.
"Na fita kasuwa da hantsi amma ban bi ta wurin ba saboda an rufe wurin ana aikin ceto," ta sanarwa Legit.ng Hausa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel