Yan kasar Nijar, da wasu yan bakin haure ke aikin Okada a Legas, Kwamishanan yan sanda

Yan kasar Nijar, da wasu yan bakin haure ke aikin Okada a Legas, Kwamishanan yan sanda

  • Gwamnatin jihar Legas ta haramta aikin Okada wanda aka fi sani da babur a kananan hukumomi shida a jihar
  • Hukumar yan sandan jihar ta lashi takobin fito na fito da dukkan dan babur din da aka kama yana aiki
  • Kwamishanan yan sandan jihar ya ce mafi akasarin masu aikin babur yan bakin haure ne

Legas - Kwamishanan yan sandan jihar Legas, Abiodun Alabi, ya bayyana cewa hukumar za tayi fito-na-fito da yan bakin haure dake zuwa jihar aikin babur.

Alabi ya bayyana hakan ranar Juma'a yayin hira da kamfanin dillancin labarai (NAN) a Legas.

Ya ce hukumar na sane da wasu yan bakin haure dake aikin Okada a jihar kuma zasu damke su.

NAN ya ruwaito cewa mafi akasarin masu aiki da babur a Legas ya kasashe mau makwabtaka da Najeriya ne.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Yadda bene mai hawa 3 ya murkushe jama'a, mutum 4 sun rasu, 5 sun jigata

Cikinsu akwai yan kasar Nijar, Togo, Kotono da Chadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maus aikin Okada a Legas
Yan kasar Nijar, da wasu yan bakin haure ke aikin Okada a Legas, Kwamishanan yan sanda

Yace:

"Muna sane da cewa yan babur da yawa dake aiki a Legas yan bakin haure ne kuma mun fara bibiyarsu don katabta sunayensu."
"Zamu yi amfani da tsohon dabarar hana babur shigowa jihar. Zamu kwace duk babur din da aka gani yana kokarin shiga Legas."

Alabi ya kara da cewa yan siyasa su daina siyawa mataa babura da sunan taimaka musu.

Yawancin matukan babur na Okada yan ta'adda ne, kwamishanan yan sandan jihar Legas

Kwamishanan yan sandan jihar Legas, Abiodun Alabi, ya bayyana cewa yawancin matasa masu aikin tuka babur a jihar Legas yan ta'adda ne masu aikata laifuka a fadin jihar.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da haramta tukin babur a kananan hukumomi shida a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta dakatad da dawowa aikin jirgin kasa Abuja-Kaduna sai baba ta gani

Yayin hira a shirin Sunrise Daily na tashar ChannelsTV ranar Alhamis, Kwamishanan Alabi ya bayyana cewa an kwace lasisin yan babur da yawa bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar

Asali: Legit.ng

Online view pixel