Sabuwar dokar APC ta baiwa Amaechi, Ngige awanni 72 su yi murabus ko su hakura da takararsu

Sabuwar dokar APC ta baiwa Amaechi, Ngige awanni 72 su yi murabus ko su hakura da takararsu

  • Sabuwar dokar APC na zaben 2023 zai tilasatawa wasu ministocin Shugaba Buhari guda biyu yin murabus daga kujerarsu a yan kwanaki masu zuwa
  • Ya zama dole ministan sufuri, Chibuike Amaechi da takwaransa na kwadago, Chris Ngige su hakura da mukamansu idan har suna son su gaje ubangidansu a 2023
  • Su dukkansu biyu dai sun nuna sha’awarsu na neman kujerar shugaban kasar Najeriya a zaben 2023 mai zuwa

Abuja - Wata sabuwar doka da shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) suka saki a ranar Talata, ta tanadi cewa ya zama dole duk masu mukaman siyasa da ke da niyan shiga zaben fidda gwaninta a dukkan matakai su yi murabus akalla kwanaki 30 kafin zaben.

Bisa ga sabuwar dokar, wasu daga cikin yan majalisar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke neman takarar shugaban kasa kamar su ministan sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi da takwaransa na kwadago, Chris Ngige, suna da sauran kwanaki uku kacal su yi murabus ko su hakura da takararsu.

Kara karanta wannan

Tashin Bama-Bamai: Ya Zama Dole Ƴan Najeriya Su Fara Kare Kansu, In Ji Ƙwararru a Ɓangaren Tsaro

Sabuwar dokar APC ta baiwa Amaechi, Ngige awanni 72 su yi murabus ko su hakura da takararsu
Sabuwar dokar APC ta baiwa Amaechi, Ngige awanni 72 su yi murabus ko su hakura da takararsu Hoto: @SenChrisNgige
Asali: Twitter

Hakan ya kasance ne duba ga cewa zaben fidda gwanin shugaban kasa na APC, zai gudana a tsakanin ranar 30 ga watan Mayu da 1 ga watan Yuni kamar yadda yake a jadawalin jam’iyyar mai mulki.

Har ila yau, sabuwar dokar ta kawo karshen kudirin takarar wasu masu neman tsayawa takarar wasu kujeru da basu yi murabus daga mukamansu ba har zuwa ranar 25 ga watan Afrilu, jaridar The Guardian ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda yake a jadawalin jam’iyyar APC, za a gudanar da zaben fidda yan takarar Gwamna, sanata, majalisun jiha da na dokoki na jam’iyyar a tsakanin 18 da 23 ga watan Mayu, wanda hakan ne nufin masu neman kujerun da basu yi murabus ba sun rasa damar da suke da ita na shiga zaben fidda gwanin.

Jami'in APC ya yi karin haske kan sabuwar dokar

Kara karanta wannan

Ramadan: Tinubu, Nyako da jiga-jigan APC 15 da za su yi buda baki tare da Buhari a yau

Rahoton ya kuma ce wani jami’in jam’iyyar wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da ci gaban, yana mai cewa masu neman takarar shugaban kasa da ke rike da mukamai daban-daban na da dama har zuwa 30 ga watan Afrilu domin yin murabus daga mukamansu.

Jami’in ya kuma bayyana cewa yan takarar gwamna da ke rike da mukaman gwamnati da basu yi murabus ba kafin ranar 18 ga watan Afrilu basu da damar shiga takarar kujerar gwamnan kowace jiha.

Ya ce:

“Ga masu neman shiga takarar zaben fidda dan takarar shugaban kasa, suna da sauran kwanaki hudu daga yau Talata domin sauka daga mukamansu saboda dokar zabe da yace dole su aikata hakan kwanaki 30 kafin zaben fidda gwani na shugaban kasa wanda za a yi a ranar 30 ga watan Mayu.
“Wadanda ke hararar kujerar gwamna da basu aikata hakan ba sun fita daga tseren saboda an shirya gudanar da zaben fidda gwanin gwamnoni a ranar 18 ga watan Mayu. Hakan ya yi daidai da dokokin da aka gindaya.”

Kara karanta wannan

Martanin yan Najeriya kan sabuwar wakar sukar gwamnatin Buhari da Rarara ya yi

Da wannan sabuwar doka da lokacin da aka bayar na yin murabus, ministan shari’a kuma atoni janar na tarayya, Abubakar Malami, wanda aka ce yana neman takarar kujerar gwamnan jiharsa ta Kebbi, ya rasa damarsa, domin kai tsaye sabuwar dokar ta soke takararsa.

Shirin 2023: Ali Ndume, Suswam da jiga-jigai 5 da ke aiki don ganin wasu 'yan takara sun gaji Buhari

A gefe guda, mun ji cewa yayin da Najeriya ke shirye-shiryen babban zabenta na 2023, wasu yan siyasa sun nada wadanda za su jagoranci yakin neman zabensu.

Yan siyasa a fadin jam’iyyun siyasa daban-daban suna ta tallata ubannin gidansu domin ganin sun zama yan takarar jam’iyyunsu mabanbanta.

A cikinsu akwai manyan sanatoci, gogaggun ‘yan siyasa da kuma tsofaffin masu rike da mukaman siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel