Yadda Lauyoyin Mala Buni suka shirya makarkashiya domin yakar APC inji El-Rufai

Yadda Lauyoyin Mala Buni suka shirya makarkashiya domin yakar APC inji El-Rufai

  • Malam Nasir El-Rufai ya bayyana dalilin da ya sa wasu Gwamnonin APC suka tsige Mai Mala Buni
  • A wata hira da aka yi da shi, Gwamna Nasir El-Rufai ya ce lauyoyin Buni sun nemi kawo cikas a APC
  • An yi yunkurin zuwa kotu domin a hana APC ta shirya zaben ta na shugabannin jam’iyya na kasa

Abuja - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana cewa sun gano akwai shirin dakatar da zaben shugabannin jam’iyyar APC na kasa da za ayi.

Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa gwamnoni sun fahimci lauyoyin Mai Mala Buni da wasu masu goyon bayansu ne suka shirya wannan zagon-kasa.

Da ya bayyana a shirin ‘Politics Today’ a gidan talabijin na Channels Television, Gwamnan na Kaduna ya fayyace dalilin sauke Gwamna Mai Mala Buni.

Kara karanta wannan

Rikicin gida: Gwamnoni 6 da suka shiga suka fita, har suka ga bayan Mai Mala Buni a APC

A cewar El-Rufai, lauyoyin tsohon shugaban na APC sun so suyi amfani da kotu domin samun umarnin hana zaben shugabannin da aka shirya za ayi.

Za a jefa APC a matsala

Gwamna El-Rufai ya bayyana cewa sake dakatar da zaben zuwa watan Mayu zai zo daidai da lokacin da INEC ta bada domin fito da ‘dan takarar 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Punch ta rahoto Malam El-Rufai yana cewa tun a watan Nuwamban 2021 wasu lauyoyi suka kalubalanci APC a kotu, amma Buni bai yi komai ba.

El-Rufai
Malam Nasir El-Rufai Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Abin har ta kai bakin lauyoyin Buni ya zo daidai da na wadanda suka kai karar jam’iyya. Hakan ta sa wasu gwamnonin suka ce ya zama dole a dauki mataki.

“Mun gano hukuncin kotun a shekarar bara. A Nuwamba aka zartar da shi. Wani ‘dan jam’iyya ya je kotu, ya ce ka da ayi zabe sai an gama shari’a.”

Kara karanta wannan

Wata sabuwa a APC, an samu Sanatoci sun ce ba a tunbuke Mala Buni daga matsayinsa ba

“Kafin a kammala shari’ar da jam’iyya, za a iya daukar watanni ko shekaru, sai lauyoyin Buni suka je kotu, su ka amince da karar da aka shigar.”
“Babu wanda ya san da wannan kara. Boyayyan nukiliya ne aka shirya domin ruguza zaben shugabanni, sai muka yarda akwai ‘yan zagon-kasa.”
“Idan ba mu yi zaben shugabanni ba, aka samu aka fito da ‘yan takara, ‘yan takarar mu za su iya rasa kujerunsu duka kamar yadda aka yi a Zamfara.”

Rawar da Gwamnoni 6 suka taka

Kun ji cewa wasu Gwamnonin APC akalla 6 ne suka yi sanadiyyar da Mai Mala Buni ya rasa kujerar shugaban jam’iyya bayan sun yi zama da Shugaban kasa.

Gwamnonin su ne na jihohin Ekiti, Jigawa, Filato, Kebbi, Neja da kuma shi na jihar Kaduna. Daga cikinsu aka zabi wanda ya zama shugaban APC na rikon kwarya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel