Doka: Dole ne duk mai son ganawa da Buhari ya yi gwajin Korona saboda dalilai

Doka: Dole ne duk mai son ganawa da Buhari ya yi gwajin Korona saboda dalilai

  • Gwamnati ta sake sanya sabuwar dokar Korona, inda tace dole ne masu ziyartar fadar shugaban kasa su yi gwajin Korona
  • Wadanda dokar ta shafa sun hada da gwamnoni da duk wasu manyan mutanen da za su gana da jami'an gidan gwamnati
  • Sai dai, shugabannin da suka fito daga waje ba a bukatar suyi wannan gwaji na Korona, duk da ana shawartar suyi hakan

Abuja - Za a bukaci masu ziyara a fadar shugaban kasa da ke Abuja, su yi gwajin Korona kafin a ba su izinin shiga fadar mulkin kasar, wacce aka fi sani da Aso Rock, ko dai don ziyartar shugaban kasa ko kuma wani jami'i.

Wadanda abin ya shafa sune muhimman mutane ciki har da gwamnoni.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sace wasu mata a Kaduna ranar jajiberin sabuwar shekara

Sabuwar dokar a cewar babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Malam Garba Shehu, za ta bukaci duk wani bako da ya yi gwajin kyauta a kofar shiga Villa.

Sabuwar dokar Korona a Villa
Doka: Dole ne duk mai son ganawa da Buhari ya yi gwajin Korona saboda dalilai | Hoto: Buhari Sallau
Asali: Twitter

Duk da haka, ya ce an kebe wasu shugabannin da suka fito daga waje daga dokar, ko da yake ana shawararsu da yin gwajin saboda tsaro, Daily Trust ta ruwaito.

"Eh, an sanya sabon tsarin Korona ga duk masu ziyara a Villa, ba ga gwamnoni kadai ba.
“Kowane mai ziyara a Villa, ba kawai wadanda ke ganin Shugaban kasa ba, yanzu ana bukatar yin gwajin gaggawa a kofar shiga.
“Ana ba da kayan gwajin kyauta don haka ba a bukatar kowa ya biya. Wannan na dan lokaci ne kawai idan aka yi la'akari da hauhawar kwanan nan, kuma za a cire shi duk lokacin da lamarin ya kare."

Kara karanta wannan

Dokar hana babura: 'Yan Kaduna sun kagu a dage dokar hana babura bayan watanni uku

Garba Shehu ya bayyana wannan matakin da nufin dakile yaduwar Korona a fadar shugaban kasa da ma kasa baki daya.

A makwannin biyu da suka gabata ne aka samu yaduwar Korona a fadar shugaban kasa, inda ministoci da hadimin Buhari suka kamu da cutar.

Wannan sabuwar doka dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Garba Shehu ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa ya murmure daga cutar Korona da ya ke yi.

An hana wuraren ibada da gidajen shakatawa a Abuja taro

A wani labarin daban, a wani bangare na kokarin ganin an kiyaye dokar lafiya, hukumar babban birnin tarayya Abuja ta sanar da haramtawa wuraren shakatawa da bukukuwa da majami’u na addini da ke da mabiya sama da 50 yin taro.

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, 25 ga Disamba, ta ce an sanar da matakin ne sakamakon sake barkewar Korona.

Kara karanta wannan

Na warke daga cutar COVID-19, Kakakin Buhari, Garba Shehu

Hakazalika, gwamnati ta ce gazawar mazauna Abuja wajen daukar matakan kariya masu sauki abin damuwa ne ga lafiyar al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel