EFCC ta cigaba da gabatar da hujjoji a kotu da za su sa a daure tsohon gwamna Fayose

EFCC ta cigaba da gabatar da hujjoji a kotu da za su sa a daure tsohon gwamna Fayose

  • EFCC ta na zargin Ayo Fayose da karbar $5m (kusan Naira biliyan 1.8) a hannun Musliu Obanikoro
  • Hukumar ta na zargin tsohon gwamnan da sayen gidaje na miliyoyin kudi ta hannun wani na kusa da shi
  • Lauyoyin EFCC sun gabatar da wata shaida da ta fadawa kotu yadda aka saye wasu gidaje a hannunta

Lagos - An cigaba da shari’ar da ake yi tsakanin hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa da tsohon gwamna Ayodele Fayose.

Hukumar dillacin labarai na kasa, ta kawo rahoto cewa an yi zama a kotun tarayya da ke Legas a jiya ranar Laraba, 1 ga watan Disamba, 2021, kan wannan shari’a.

EFCC ta kira wata Joanne Tolulope a matsayin shaida na 11, wanda ya yi bayanin yadda na-kusa da Ayo Fayose, Abiodun Agbele ya saye gida na miliyoyin kudi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin daka tsige DPO daga kujerarsa bisa zargin kashe dan bindiga

Rotimi Jacobs SAN ne lauyan da ya gabatar da shaidan da aka kawo, wanda ta fadawa Alkali cewa Agebele ya saye chalets a kamfaninta na Still Earth Ltd a 2015.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta fitar da rahoto, wannan kamfani na Still Earth Ltd ya na harkar saye da saida gidaje ne kuma da gyaran gidaje a Najeriya.

Tsohon gwamna Fayose
Dino, Fayose da Saraki @Democratic Movement
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar shaidar da EFCC ta gabatar, Mista Agbele ya kira ta a wayar salula tsakanin Maris zuwa Yulin 2015, ya tambaye ta ko akwai wani gidan saidawa a kasa.

Yadda mu ka yi cinikin gidaje - Joanne Tolulope.

“Aka yi dace, mu na da gidaje a kasuwa; mu ka yi maganar sa lokacin da Agbele zai je ya duba gidan. Ya zo cikin watan Maris na 2015, ya na neman gidaje biyu, ya biya Naira miliyan 575 domin mallakar gidajen.” - Joanne Tolulope.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan Ya Zama Dan Gudun Hijira, In Ji Gwamnan Bayelsa

Alakar kasuwancin ta da wannan na kusa da gwamna bai kare ba, Agbele ya sake dawowa a watan Yuli inda ya biya Naira miliyan 573 domin sayen wasu gidajen.

A game da yadda aka biya kudin kuwa, Tolulope ta ce an fara aika mata N800m ne daga asusun De Privateer Ltd., sai aka aiko wani mutumi da ya kawo mata N200m.

Capital Field Investment and Trust Ltd., sun aiko mata da N105m, sai kamfanin Hoss Concept ya turo N39.5m, yayin da N40m suka fito daga kamfanin De Privateer Ltd.

Lauyoyin gwamnatin Kano sun yi rashin sa'a

A makon nan ne aka ji yadda lauyoyin gwamnatin jihar Kano su ka sha kashi a manyan shari’a uku a cikin ‘yan watannin nan, daga ciki akwai shari'arsu da Jafar Jafar.

Haka zalika an ba Muhammadu Sanusi II gaskiya a shari'arsa da gwamnatin Kano. Amma gwamnati tace za ta daukaka kara, domin ba ta yarda da hukuncin ba.

Kara karanta wannan

Abba Kyari: Yadda na Biya Cin Hanci Wajen Shigo da Hodar Iblis Inji Shaida a Kotu

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel