Yanzu-yanzu: An hana ma'aikatan gwamnati shiga ofis don basu yi rigakafin Korona ba

Yanzu-yanzu: An hana ma'aikatan gwamnati shiga ofis don basu yi rigakafin Korona ba

  • Gwamnatin taraya ta cika alkawarinta na hana wadanda basu yi rigakafn Korona shiga ofisoshinsu
  • Jami'an tsaron sun zagaye ofishoshin da sassafe don hana ma'aikatan da basu yi rigakafin ba shiga
  • Wadanda suka gabatar da hujjar cewa basu da Korona kuma za'a barsu

Abuja - Jami'an tsaro sun hana ma'aikatan gwamnatin da ba suyi rigakafin Korona ba shiga ofishoshinsu a sakatariyar gwamnati dake birnin tarayya Abuja, rahoton Punch.

Wadanda basu yi rigakafin ba amma suka gabatar da takardar shaidar gwajin Korona PCR da ya nuna basu da cutar zasu shiga.

Kungiyar ma'aikatan gwamnatin tarayya ta yi kira ga Gwamnati ta dage wannan doka zuwa watan Maris 2022.

A riwayar ChannelsTV, misalin karfe 7 na safe jami'an tsaro suka mamaye kofar shiga sakatariyar gwamnati kuma suka bukaci kowa ya nuna hujjar cewar yayi rigakafi ko bai da Korona.

Kara karanta wannan

Bayan kusan shekaru 2 suna zaune gida suna diban albashi, Gwamnati tace ma'aikatanta su koma aiki

Omicron: An hana ma'aikatan gwamnati shiga ofis
Yanzu-yanzu: An hana ma'aikatan gwamnati shiga ofis don basu yi rigakafin Korona ba Hoto: https:/punchng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk ma'aikacin da bai yi rigakafin Korona ba nan da kwanaki 10 ba zai shiga Ofis ba

A baya mun kawo muku rahoton cewa gwamnatin tarayya ta jaddada cewa duk ma'aikacin gwamnatin da bai yi rigakafin Korona nan da ranar 1 ga Disamba ba, ba zai samu damar shiga ofishinsa ba.

Sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana hakan ranar Juma'a a Abuja yayin taron kamfen din yiwa mutane rigakafin.

Adadin wadanda aka yiwa rigakafi kawo yanzu

Shugaban hukumar cigaban kananan asibitoci (NPHCDA), Dr Faisal Shuaib, ya bayyana adadin yan Najeriya da aka yiwa rigakafi kawo yanzu.

A cewarsa, kawo ranar 19 ga Nuwamba, yan Najeriya 5,989,480 suka yi allurar farko, yayinda mutum 3,341,094 suka yi alluran biyu gaba daya.

Tsoron Omicron

Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya, NCDC ta tabbatar da bullar nau'in cutar korona na Omicron da ke firgita kasashen duniya.

Kara karanta wannan

Garba Shehu: Buhari ya cancanci jinjina kan yadda ya shawo kan matsalar tsaro

Hukumar ta ce an gano mutane biyu da ke dauke da nau'in cutar a halin yanzu.

Dr Ifedayo Adetifa, Direkta Janar na hukumar ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa.

NCDC ta ce an gano nau'in cutar biyu ne ta hanyar amfani da fasahar gano tsarin kwayar halita ta 'genomic sequencing'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel