Dattawan Arewa sun gargadi Buhari kan yi wa Nnamdi Kanu afuwa, sun bada dalilinsu

Dattawan Arewa sun gargadi Buhari kan yi wa Nnamdi Kanu afuwa, sun bada dalilinsu

  • Kungiyar Arewa Consultative Forum ta ce ba ta goyon bayan a fito da jagoran IPOB, Nnamdi Kanu
  • Dattawan na yankin Arewa sun ce babu dalilin ayi watsi da shari’ar Nnamdi Kanu da ke gaban kotu
  • Emmanuel Yawe ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta bar kotu ta yankewa Kanu hukuncin da ya dace

Nigeria - Kungiyar Arewa Consultative Forum ta dattawan Arewacin Najeriya tace bai dace ayi wa shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu afuwa ba.

Sakataren yada labarai na kungiyar ACF, Emmanuel Yawe yace ba za a iya yarda da Nnamdi Kanu ba, don haka ya ja-kunne a kan gwamnati ta yafe masa.

Emmanuel Yawe ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi hira da Jaridar Punch a ranar Litinin.

Babban jigon na kungiyar dattawan Arewa yace abin da ya kamata shi ne a bar shari’a tayi aiki tun da gwamnatin Najeriya ta na aiki ne da tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Aisha Yesufu ga majalisar dokoki: Ku tsige Buhari, har 'yan Arewa sai sun ji dadin haka

“Ya za ayi da karar shi (Nnamdi Kanu) a kotu? Za ayi fatali da shari’ar? Idan shi (Buhari) ya fito da shi, an gama shari’ar kenan? - Emmanuel Yawe.
"Damukaradiyya muke aiki da shi, akwai tsarin mulki, an raba iko tsakanin bangaren shari’a da na zartarwa. Idan an kai mutum kotu, a bar shi da alkali."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dattawan Ibo
Buhari da manyan Ibo Hoto: ait.live
Asali: UGC

“Shugaban kasa wanda yake bangaren zartarwa ba zai iya kai batu gaban kotu ba, sai kuma ya zartar da hukunci ta hanyar kyale wanda ake zargi.”

Yawe yace kungiyar ACF ta na so a bar dokar kasa da tsarin mulki su yi aiki a kan ‘dan tawaren.

Kanu bai da tabbas - ACF

“Da aka sake kama Kanu, mun yi gargadi cewa ka da a zalunce shi a kotu, mun nemi ayi masa shari’a ta gaskiya. Yanzu kuma ana cewa a fito da shi.”

Kara karanta wannan

Kotu tayi fatali da karar da aka shigar a kan kudin Janar Abacha da aka dawo da su a 2020

“Ta ya za ka yarda da wanda ya karbi beli, ya tsere, kuma aka damke shi. Sanata ya tsaya masa, amma ya ki bayyana da ake shari’a a kotu.” – Yawe.

Yawe ya maida martani ne ga wasu daga cikin dattawan kasar Ibo da suka je wajen shugaban kasa su na neman afuwar shugaban 'yan tawaren na IPOB.

A baya an ji cewa wani jami'in DSS ya bayyana cewa, a halin yanzu ana kokarin dawo da Sunday Igboho kasar nan domin fuskantar hukuncin da yake kansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel