Hukumar NYSC ta koka kan kudin abinci: N650 ga 'yan NYSC, N1000 ga fursunoni

Hukumar NYSC ta koka kan kudin abinci: N650 ga 'yan NYSC, N1000 ga fursunoni

  • Hukumar NYSC ta koka kan yadda gwamnati ta amince da kudaden abinci ga fursunoni wanda ya fi na 'yan bautar kasa na NYSC a kasar
  • Gwamnati ta amince da biyan N1000 ga kowane fursuna da aka tsare a gidan gyaran hali, yayin da NYSC bai kai haka ba
  • Wannan yasa NYSC ta ce ya kamata a kara, duba da an amince masu laifi su ci mai kyau fiye da na wadanda suke yi wa kasa hidima

Abuja - Hukumar NYSC ta koka kan yadda fursunonin da ke karkashin kulawar ma’aikatun hukumar gyaran jiki ta Najeriya ke samun na abinci fiye da na ‘yan NYSC.

Babban Darakta Janar na NYSC, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim, wanda ya bayyana haka a lokacin da ya bayyana a gaban wani kwamitin majalisa don kare kasafin kudi a ranar Larabar da ta gabata, ya ce ana ba 'yan NYSC abincin da ya kai na N217.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Anambra: DG na NYSC ya ziyarci rumfunan zabe, ya yabawa 'yan bautan kasa

Don haka, ya bukaci Majalisar Wakilai da ta samar kari a kason abinci a kasafin kudin shirin na 2022.

Yadda gwamnati ke kashewa fursunoni N1000, N650 kuma ga 'yan bautar kasa
Shugaban hukumar NYSC | Hoto: thecable.ng
Asali: Facebook

A ranar 27 ga Oktoba, 2021 ne kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin cikin gida ya kara yawan kudin ciyar da fursunoni daga naira 450 da take ba kowane mutum a yanzu zuwa mafi karancin naira 1,000 a kowace rana.

Jami’an NCS sun kasance a majalisar dattawa domin kare kasafin kudin hukumar na 2022, inda suka bada shawarar a kara kudaden ciyarwar a rana zuwa N750.

Kwamitin, ya bayyana adadin a matsayin wanda bai isa ba kuma ya kara yawansa daidai da yanayin tattalin arzikin da ake ciki a yanzu, inda ya yi alkawarin yin nazari a kan kudin ciyar da fursunoni daga N450 zuwa N1000 a kowace rana.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya ce zai kafa wani tarihin da ba a taba ba a Najeriya kafin ya bar ofis

A nasa jawabin, Ibrahim, wanda ya bayyana cewa al'ada ce ta farko da ya gabatar da kasafin ga kwamitin, ya ce kasafin kudin NYSC ya ci gaba da kasancewa a yadda yake a shekarun da suka gabata.

The Cable ta ruwaito Ibrahim yana cewa:

"Kalubalenmu shi ne a fannin ciyar da abinci. Amincewa da kasafin kudin ciyar da kowane dan bautar kasa shine N650, wanda bai wadatar ba. A lokacin da za ka raba shi zuwa abinci uku (a rana), wato Naira 216 a kowane kari. Don haka muna kira ga wannan kwamiti da ta taimaka mana.
“Ko a kwanan baya ma a ma’aikatar harkokin cikin gida an kara ciyarwar fursunoni zuwa Naira 1,000. Don haka, idan har za mu iya ciyar da masu laifi da N1,000, wadanda suka kammala karatunmu suna sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa kasarmu hidima... Ina rokon wannan kwamiti ya yi wani abu a kai.”

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya yi basaja ya kai ziyaran bazata asibiti, ya damke ma'aikata na karban kudin Haram

Shugaban kwamitin, Yemi Adaramodu, a farkon jawabinsa na bude taron, ya bayyana cewa hukumar ta NYSC na cin kudaden da yawa domin ba hukumar samar da kudaden shiga ba ce, ita ce ke tafiyar da jama’a, musamman matasan Najeriya.

Zaben gwamnan Anambra: DG na NYSC ya ziyarci rumfunan zabe, ya yabawa 'yan bautan kasa

A wani labarin, Premium Times ta rahoto cewa, Babban Darakta Janar na kungiyar yi wa kasa hidima (NYSC), Shua’ibu Ibrahim, ya yabawa kishin kasa da ‘yan kungiyar da ke gudanar da aikin zaben gwamna a jihar Anambra.

Mista Ibrahim ya yi wannan yabon ne a ranar Asabar da ta gabata a lokacin da yake sa ido kan zaben a kananan hukumomi tara na jihar.

Yabon ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na NYSC Adenike Adeyemi ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari: Ya kamata gwamnati ta daina yin sabbin tituna a Najeriya bisa wasu dalilai

Asali: Legit.ng

Online view pixel