Mutane 200, 000 sun rungumi tsarin E-Naira a cikin awanni 24 da fitowa Najeriya

Mutane 200, 000 sun rungumi tsarin E-Naira a cikin awanni 24 da fitowa Najeriya

  • Kawo yanzu mutane kusan 200, 000 suka yi rajista da sabon tsarin kudin eNaira
  • Bankin CBN ya shigo da kudin yanar gizo a shirin Central Bank Digital Currency
  • Mutane da-dama sun sauke manhajar eWallet domin su fara yin ciniki da eNaira

Nigeria - A cikin sa’a 24 da aka kaddamar da kudin yanar gizon Central Bank Digital Currency (CBDC), mutane da-dama sun yi rajista a wannan tsarin.

Jaridar This Day ta fitar da rahoto a ranar Laraba cewa kimanin mutane 200, 000 suka nuna sha’awar fara amfani da alaben yanar gizo na E-Wallet.

Wadannan dinbin mutane sun sauke manhajar kudin gizon jim kadan bayan ya shigo Najeriya. Nairametrics tace manhajar na ta karbuwa a PlayStore.

Mutane sama da 156,700 suka yi rajista domin su yi amfani da wannan alabe. Bayan haka akwai mutum fiye da 23, 000 da suka yi rajista a matsayin dillali.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Alkaluman sun nuna yadda ake sha’awar tsarin, kuma suka rungumi wannan kudi na yanar gizo da babban bankin CBN ya shigo da shi cikin makon nan.

Ana sa rai nan da wasu ‘yan kwanaki kadan, mutanen da za su sauke manhajar eNaira su karu sosai, a sanadiyyar wayar da kan da bankin CBN zai rika yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutane 200, 000 sun rungumi tsarin E-Naira a cikin awanni 24 da fitowa Najeriya
Ana kaddamar da eNaira a Aso Villa Hoto: @bashahmad
Asali: Facebook

CBDC zai bunkasa tattalin Najeriya?

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace ana hasashen jimillar tattalin arzikin kasa na GDP zai kai fam Dala biliyan 29 nan da shekaru goma masu zuwa.

“Babu shakka hasashe ya nuna rungumar CBDC da fasahar blockchain zai sa karfin tattalin arzikin Najeriya ya kai $29b nan da shekaru goma.” – Buhari.

Najeriya ta ciri tuta a Afrika

A cewar Mai girma Muhammadu Buhari, Najeriya ce kasar Afrikar farko da ta rungumi kudin ta na yanar gizo. Har yanzu wannan tsari bai ratsa Duniya ba.

Kara karanta wannan

Da dumi: Shugaba Buhari ya kaddamar da kudin e-Naira tare da Gwamnan CBN

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele yace eNaira zai bunkasa tattalin daga haraji, ya sa kudi su rika yawo, kuma ya rage abin da ake kashewa wajen buga Naira.

An dade ana aiki a kan eNaira

Kwanaki babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da cewa zai kaddamar da tsarin gwajin kudi na shafin yanar gizo da aka yiwa lakabi da eNaira a watan Oktoba.

Tun a shekarar 2017, gwamnatin Najeriya ta fara aiki a kan tsarin CBD, sai yanzu abin ya tabbata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel