Bayan watanni 6 da samun kujerar WTO, har ana jita-jitar Okonjo-Iweala za tayi murabus

Bayan watanni 6 da samun kujerar WTO, har ana jita-jitar Okonjo-Iweala za tayi murabus

  • Rade-radin da yake yawo shi ne Ngozi Okonjo-Iweala za ta ajiye aikin WTO
  • Tsohuwar Ministar Najeriyar ta karyata wannan, tace tana jin dadin aikinta
  • Dr. Okonjo-Iweala tace ba ta da wata sha’awar tsayawa takara a zaben 2023

Geneva - Jita-jita suna ta yawo cewa shugabar kungiyar WTO, Ngozi Okonjo-Iweala, tana tunanin ajiye aikinta, ta rubuta murabus bayan watanni da shiga ofis.

Rahotanni daga Bloomberg sun ce Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta soma gajiya da aikin WTO, har ta fara kawo a ranta za ta ajiye aikin idan ta rasa yadda za tayi.

Wasu majiya daga WTO sun bayyana cewa Ngozi Okonjo-Iweala ta fara kawo batun yin murabus.

Okonjo-Iweala ta shaida wa wasu jakadu da ma’aikatan kungiyar WTO cewa za ta iya barin aiki kwatsam, tace tun da ta shiga ofis ba ta saye kaya a gidanta ba.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa na kira Tinubu 'Shugaban kasa' a kasar waje - Dan majalisa yayi bayani kan bidiyon da ya bazu

Idan Okonjo-Iweala ta ajiye aiki a wannan yanayi, jaridar The Cable tace WTO ta shiga karin matsala. John Denton yana ganin hakan zai taba kasashen Duniya.

Shugabar WTO ta 7
Ngozi Okonjo-Iweala Hoto: www.wto.org
Asali: UGC

Meyasa aiki a WTO yake wahala?

Shugabannin kungiyar WTO sun saba fuskantar kalubale saboda yadda ake aiki. Dole duka ‘ya ‘yan wannan kungiya 164 su sa hannu kafin a iya kowane irin aiki.

WTO tana fama da sabani, rabuwar kai da rashin yadda tsakanin shugabanninta. Haka zalika dokokin aiki a kungiyar kasuwancin Duniyar suna da tsauri sosai.

Ba gaskiya ba ne - Dr. Okonjo-Iweala

Amma Dr. Okonjo-Iweala ta musanya wadannan jita-jitan da suke ta yawo. Tsohuwar Ministar tattalin arzikin ta shaida wa ‘yan jarida cewa tana jin dadin aikinta.

Jita-jitar da ake yi shi ne bayan ta yi murabus a WTO, Dr. Okonjo-Iweala tana sha’awar neman kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023 da za ayi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi fatali da bukatar Ndume ta zare hannunsa daga shari'ar Maina

“Zuwa na nan kenan. Ina jin dadin abin da nake yi. Aiki ne mai dadi, ina kokarin cin nasara a nan.”

A watannin baya ne aka ji tsohuwar ministar kudin Najeriya, Dr Ngozi Okonjo Iweala ta zama sabuwar Darakta Janar na kungiyar kasuwancin na duniya.

Ngozi Okonjo Iweala ta zama mace ta farko kuma bakar fata da ta dare kan wannan kujera.

Asali: Legit.ng

Online view pixel