Majalisar Dattawa za ta kawo doka mai tsauri da za ta kawo karshen garkuwa da mutane

Majalisar Dattawa za ta kawo doka mai tsauri da za ta kawo karshen garkuwa da mutane

  • Sanata Ibikunle Amosun ya kawo kudirin da zai yaki masu garkuwa da Bayin Allah
  • Idan kudirin ya zama doka, za a rika yanke wa masu yin laifin hukuncin rai da rai
  • Ibikunle Amosun yace dokokin da ake da su a yanzu ba za su iya magance laifin ba

Abuja - A ranar Talata, 21 ga watan Satumba, 2021, Sanatoci suka kawo wani kudiri da zai sa a kara daukar mataki mai tsauri a kan masu garkuwa da mutane.

Daily Trust tace kudirin zai yaki miyagun ‘yan bindiga da duk wanda aka kama yana satar mutane da karfi da yaji, ya tsare su, ko yana karbar kudin fansa.

Majalisar dattawa ta yi wa kudirin da take da 'Abduction, Wrongful Restraints and Confinement Bill 2021' wanda ya yanke hukuncin daurin rai ga masu wannan laifi.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Arewa maso yamma ta rikice, kiyasin mu ya na kai da kai da Afghanistan

Rahoto yace kudirin ya tsallake matakin sauraro na biyu a majalisar tarayyan. Kudirin yana neman a daure duk wanda ya ci kudin satar mutane na shekaru 30.

Meyasa muka kawo kudirin? - Sanata Ibikunle Amosun

Sanata Ibikunle Amosun (APC, Ogun) da ya shigo da maganar yace kudirin zai share dokokin da ake da su a baya, zai taimaka wajen yaki da garkuwa da mutane.

A dokar da ake da ita mai-ci, mafi tsaurin hukuncin da za a iya yanke wa wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane shi ne zaman gidan yari na shekaru 10.

Senator Ibikunle Amosun
Sanata Ibikunle Amosun Hoto: Ibikunle Amosun
Asali: Facebook

Ibikunle Amosun yana ganin wannan doka ba ta taimaka wajen kawo karshen danyen aikin ba.

“Domin a koya masu laifi hankali, an kawo daurin rai da rai ga masu garkuwa da mutane, musamman idan laifin ya kai ga rasa rai.”

Kara karanta wannan

Ina tabbatar muku za'a hukunta tubabbun yan Boko Haram: Kwamandan Operation Hadin kai

“An kara wa dokar tsauri ta yadda duk wadanda suka amfana da abin da aka samu daga satar mutane, za su yi shekaru 30 a gidan yari.”

Sanatan ya koka game da yadda masu wannan aika-aika suke jawo mutuwar Bayin Allah da kuma karya dukiyar al’umma, yace talakawa abin ya fi shafa a yanzu.

An kama masu ba 'yan bindiga abinci

Bayan dakile layukan waya, a jiya aka ji cewa 'yan sandan jihar Katsina sun damke mutane biyar da ake zargin suna taimaka wa 'yan bindiga da man fetur da burodi.

A daidai wannan lokaci ne kuma jami’an tsaro suka yi ram da wani gurgu a cikin tawagar ‘Yan bindiga a Katsina. Rundunar 'yan sandan jihar ta bayyana haka a jiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel