Wole Soyinka: Akwai cakwakiya idan aka san gaskiyar yadda aka yi ram da Nnamdi Kanu

Wole Soyinka: Akwai cakwakiya idan aka san gaskiyar yadda aka yi ram da Nnamdi Kanu

  • Farfesa Wole Soyinka ya yi Allah-wadai da yadda aka kama Nnamdi Kanu
  • Masanin ya ce gwamnati ta saba doka wajen cafke shugaban kungiyar IPOB
  • A na sa ra’ayin, ya kamata jami’an tsaro su soma da Miyagun ‘Yan bindiga

Fitaccen Farfesan Najeriya, kuma shahararren marubucin Duniya, Wole Soyinka, ya yi tir da salon da aka bi wajen kama shugaban IPOB, Nnamdi Kanu.

Babban marubucin ya zargi gwamnatin tarayya da shugaba Muhammadu Buhari yake jagoranta da yin garkuwa da Nnamdi Kanu daga inda yake a ketare.

Farfesan ya bayyana hakan da BBC Pidgin ta yi hira da shi a ranar Litinin, 5 ga watan Yuli, 2021.

KU KARANTA: Dokubo Asari ya dura kan Nnamdi Kanu

A cewar Wole Soyinka, hayaniya za ta kicime idan har aka yi wa ‘yan kasa cikakken bayanin gaskiyar yadda aka cafko Kanu daga kasar wajen da yake.

Jaridar The Cable ta rahoto yadda hirar ta kasance:

Idan aka san gaskiya, sama da kasa za su hade

“Ba aiki na ba ne in fada wa shugaban kasa ya shirya, domin ko ina zai amsa a lokacin da gaskiyar kamun Kanu ya fito fili.”
“Mutane suna ta ‘yan surutai, a ce wannan, kuma ace wancan. Ana kokwanton ko Najeriya ta bi dokokin kasashen ketare.”
Wole Soyinka: Akwai cakwakiya idan aka san gaskiyar yadda aka yi ram da Nnamdi Kanu
Farfesa Wole Soyinka Hoto: dailypost.ng
Asali: Facebook

KU KARANTA: Jonathan zai samu lambar yabon Africa Advancement Forum

Shi ma Nnamdi Kanu ya rika sakin bakinsa - Soyinka

“Abu na biyu shi ne abubuwan da Kanu ya rika yi a wajen kasar nan. Ya yi ta furta kalaman batanci, wanda hakan abin takaici ne daga gare sa.”

Sai dai inda za a samu matsala shi ne, dokar kasa ce kurum za ta iya hukunta laifin kalaman batanci.

"Ya dace ayi garkuwa da shi? Za a iya cewa ram da shi aka yi, amma garkuwa da shin aka yi. Hakan ya saba dokar waje, ya ci karo da abin da ya kamata.”

Farfesa Soyinka ya ce gwamnatin tarayya ta gaza cafke ‘yan bindigan da su ke yi wa mutane barna, amma ta iya wuf ta kama shugaban na kungiyar IPOB.

Soyinka ya ce tun farko ya kamata a ce shugaba Muhammadu Buhari ya yi maganin irinsu Miyetti Allah, ba sai daga bayan nan zai ce zai ce zai casa su ba.

A yau ne mu ka ji Sanata Abdullahi Adamu ya na cewa burin masu kururuwar Najeriya ta watse, su karbi mulkin kasar nan bayan wa'adin Muhammadu Buhari.

Tsohon Gwamnan na Nasarawa ya ce ana huro wuta ne saboda a hana Arewa yin mulki bayan 2023, Adamu ba ya ganin an danne wasu yankin a mulkin APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel