Muna kashe N30bn na tallafin wutan lantarki ga yan Najeriya kowace wata, FG

Muna kashe N30bn na tallafin wutan lantarki ga yan Najeriya kowace wata, FG

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kowani wata sai ta kashe akalla bilyan talatin don biyan kudin tallafin wutan lantarkin da yan Najeriya ke amfani da shi.

Ta kara da cewa ta rage kudin tallafin da N20bn sabanin N50bn a baya saboda cigaban da aka samu wajen amsan kudin wuta da Discos ke yi.

Gwamnati ta bayyana hakan ne a takardar da ta saki kan cigaban da aka samu a bangaren wutan lantarki a Najeriya, rahoton Punch.

Bayani kan halin da sashen lantarki ke ciki a Najeriya yanzu, gwamnatin tace,

"An kara farashin wutan lantarki da kashi 36% daga Satumban 2020. Kuma an samu karin biyan kudi da kashi 60%."
"An rage kudin tallafin da gwamnati ke biya da N20bn a wata. An samu kudi N65bn a Disamba 2020 sabanin N39bn da ake samu a baya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta kara kudin wutan lantarki ba tare da sanar da yan Najeriya ba, Bincike

DUBA NAN: Najeriya ce kan gaba a yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin Sahara - Ministan Ilimi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kowani wata muna kashe N30bn kan lantarki
Kowani wata muna kashe N30bn na tallafin wutan lantarki ga yan Najeriya, FG Hoto: Engr Saleh Mamman
Asali: Facebook

DUBA NAN: Ina PDP, ba zan yi butulci ba, ba zan koma APC ba: Mataimakin gwamnan Zamfara

Ya kamata a kara farashin wutan lantarki a Najeriya, yayi arha da yawa

Bankin duniya ta ce harajin da aka daura ma 'yan Najeriya ba ya nuni da irin kudin da kamfanin samar da lantarki da kuma kamfanin da take rarraba wutan.

An bayyana hakan ne a cikin rahoton 'Bangaren sake fasali' wanda Bankin Duniya ya fitar a ranar Talata, cewa an kashe sama da tiriliyan N1.68 a kan karin mafi karanci kudin harajin wuta daga shekaran 2015 zuwa 2019 wanda Shugaban kasa yayi.

Babban Bankin Duniya ya ce kashi 40% na masu hannu da shuni a Najeriya su ke cin kashi 80% na kudin haraji da ake kashewa.

Kara karanta wannan

'Yan fashi sun afka wa coci domin sace kudi, sun daba wa mai gadi wuka a Abuja

Asali: Legit.ng

Online view pixel