Shugaba Buhari ya fitar da danyen nadin mukami ana daf da zai bar Najeriya zuwa Landan

Shugaba Buhari ya fitar da danyen nadin mukami ana daf da zai bar Najeriya zuwa Landan

  • Emmanuel Lyambee Jime ya zama sabon babban sakataren hukumar NSC ta Najeriya
  • Nigerian Shippers Council ta na kula da kayan da aka shigo ko za a fita da su ta ruwa
  • Lyambee Jime ya rike mukamai da dama a gwamnati, kuma ya yi siyasa a shekarun da

Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da wani sabon nadin mukami a gwamnati, yayin da ya nada sabon shugaba a hukumar NSC.

Mista Emmanuel Lyambee Jime ya zama babban sakataren Nigerian Shippers Council ta kasa.

Jaridar The News ta fito da wannan labari, ta ce Emmanuel Jime zai jagoranci ragamar hukumar da ke aikin kula da jiragen fatauci da suka zo ko za su bar ruwa.

KU KARANTA: 'Yanuwa ke jawo masu rike mukaman Gwamnati su yi sata - Minista

Fadar shugaban kasa ta tabbatar da wannan rahoton a wani jawabi da mai magana da yawun Muhammadu Buhari watau Malam Garba Shehu, ya fitar a jiya.

Mukaman da Rt. Hon. Emmanuel Jime ya rike

Mista Emmanuel Jime ya yi digiri ne a bangaren shari’a, ya kuma dade ya na rike kujeru a Najeriya, bayan haka tsohon ‘dan siyasa ne da ya yi suna a Benuwai.

Kafin yanzu, Emmanuel Lyambee Jime ya taba rike kujerar manajan darekta a hukumar fita da kaya zuwa ketare, Nigeria Export Processing Zone Authority (NEPZA).

Haka zalika Jime ya wakilaci mazabar Makurdi/Guma a majalisar wakilan tarayya sau biyu, ya na majalisar tsakanin shekarar 2017, ya sauka ne bayan zaben 2015.

KU KARANTA: Yahaya Bello, Tambuwal da Gwamnoni 9 da suke harin 2023

Sabon shugaban NSC
Emmanuel Lyambee Jime Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Rt. Hon. Jime shi ne shugaban majalisar dokokin jihar Benuwai tsakanin 1992 da 1993. Bai dade a kan wannan kujera ba sai Janar Sani Abacha ya yi juyin-mulki a 1993.

Ana sa ran Hon. Emmanuel Jime zai yi shekaru hudu a ofis, wa’adinsa zai kare a tsakiyar shekarar 2025, zai iya zarcewa a wannan kujera idan shugaban kasa ya so.

Channels TV ta ce Jime ya taba neman tikitin takarar gwamnan jihar Benuwai, amma bai yi nasara ba.

Bisa dukkan alamu wannan ya na cikin matakan da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na karshe yayin da yake shirin zuwa ganin likitansa a Landan, kasar Ingila.

Shugaba Muhammadu Buhari zai sake koma wa birnin Landan a kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa. Mai magana da yawunsa,Femi Adesina, ya bayyana haka a jiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel