Kashe-kashen da ake yi ba laifin Gwamnatin Buhari ba ne, har da na mu matsalolin inji Sanatan APC

Kashe-kashen da ake yi ba laifin Gwamnatin Buhari ba ne, har da na mu matsalolin inji Sanatan APC

- Sanata Bala Ibn Na’Allah ya zauna da Shugaba Muhammadu Buhari a Aso Villa

- ‘Dan Majalisar ya hadu da Shugaban kasa ne a kan matsalolin rashin tsaro jiya

- Bala Ibn Na’Allah ya na ganin al’umma suka jefa kansu a cikin halin da ake ciki

Ba za ace gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta na da laifi kai-tsaye wajen matsalar tsaro da ake samu ba, a cewar Sanata Bala Ibn Na’Allah.

Sanatan mai wakiltar Kudancin jihar Kebbi, ya yi kira ga sauran mutanen Najeriya su taimaka wa gwamnatin tarayya wajen samar da zaman lafiya.

Bala Ibn Na’Allah ya bayyana wannan jim kadan bayan ya gana da Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa a jiya.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kona ofishin NDLEA

Jaridar Premium Times ta ce ‘dan majalisar ya bayyana cewa ya ziyarci Aso Villa domin ya yi zaman da ya saba yi da Buhari a kan sha’anin kasa.

Sanata Bala Na’Allah bai yi bayani ko ya kai wa shugaban kasar ziyara ne da sunan ‘yan majalisa ba.

Da aka tambaye sa abin da ya kawo shi, sai ya ce sun yi magana gar-da-gar da shugaban Najeriya a kan yadda za a shawo kan matsalar rashin tsaro.

Na’Allah ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnatin nan da gaske ta ke wajen kawo zaman lafiya, ya ce dole ne mutane su ba hukumomi goyon-baya.

KU KARANTA: Gwamna Ortom ya sake maidawa El-Rufai martani, ana musayar kalamai

A game da abin da ya sa matsalolin kashe-kashe suke kara bayyana har kullum, ‘dan majalisar yake cewa su ma al’umma su na da irin na su matsaloli.

“Boko Haram suna Arewa maso gabas ne, ‘Yan bindiga suna Arewa maso yamma. Wadannan duk rashin adalcin da mu ka yi a baya ne ya jawo mana su.”

Ya ce: “Abin takaici ne dai sai da gwamnatin nan ta zo wadannan abubuwa suke bayyana, shiyasa ba gwamnati ce ta ke da alhakin matsalar kai tsaye ba.”

Bayan an kashe mutum sama da 2, 000 a kwanaki 90, kun ji cewa kungiyoyi masu zaman kansu watau CSOs fiye da 120 sun ce a tsife Muhammadu Buhari.

Wadannan kungiyoyi sun bukaci shugaban kasa ya yi maganin kashe-kashen da ake yi ko a tsige shi da karfin tsiya idan har ba zai sauka ta lalama ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel