Yaron Buharin Daji da wasu ‘Yan bindiga za su bada kansu inji Matawalle

Yaron Buharin Daji da wasu ‘Yan bindiga za su bada kansu inji Matawalle

- Bello Mohammed Matawalle ya kare matsayar Gwamnatin jihar Zamfara

- Gwamna ya ce mutanen Jihar sun ga amfanin yin sulhu da ‘yan bindiga

- Matawalle yayi albishir da shirin mika wuyan wasu fitinannun tsagerun

Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara, ya ce an kammala tattauna wa da ‘dan shugaban ‘yan bindigan da aka kashe, Buharin Daji.

Daily Trust ta rahoto gwamnan ya na cewa yaron Buharin Daji, mahaifiyarsa da wani babban jagoran ‘yan bindiga a Zamfara za su ajiye makamai.

Jaridar ta ce gwamnan na Zamfara ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya zauna da tawagar shehin malamin nan na Kaduna, Ahmad Abubakar Gumi.

Ahmad Gumi ya ziyarci sansanin ‘yan bindiga a Zamfara, inda ya lallabesu, su ajiye kayan fada.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun fi sauraron Ahmad Gumi a kan gwamnati

Mai girma gwamnan ya ce matakin da ‘yan bindigan su ke shirin dauka na ajiye makaman yaki zai yi sanadiyyar samar da zaman lafiya a jihar Zamfara.

Bello Mohammed Matawalle ya ce ba don jajircewarsa ba, da ya yi watsi da sulhun da aka ayi da ‘yan bindiga, saboda akasin ra’ayin da wasu su ke da shi.

“Ana ta matsa mani lamba daga wurare da-dama saboda na yi sulhu da ‘yan bindiga, wasu sun ce ina cikinsu, wasu sun ce ina ba su kariya.” Inji Gwamnan.

Mun ga tasirin kwarai na wannan yarjejeniyar (sulhu). Kasuwannin kauyuka su na dawowa. Mun ceto mutanen da aka tsare ba tare da harbin ‘dan kowa ba.”

Yaron Buharin Daji da wasu ‘Yan bindiga za su bada kansu inji Matawalle
Gwamna Bello Matawalle Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Jami’an tsaro sun shiga jeji, sun bi Makiyaya, sun kore su a Ondo

“Idan mun san za a iya kawo karshen rikicin da karfin bindiga, da ba zamu yi sulhu ba. Za kuma mu cigaba da yin haka, duk da abin da mutane za su ce.”

Dazu kun ji Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya bayyana ainihin abin da ya jawo har ta’adin ‘yan bindiga ya yi kamari sosai a yankin Arewa maso yamma.

Malamin ya yi magana bayan ya hadu da ‘Yan bindiga a Zamfara, ya ce ta’addanci ne ba tsageranci ba.

Ahmad Gumi ya bayyana cewa rashin kula ne ya jawo wadannan mutane su ka zama gawurtattun ‘yan ta’adda, ya bada shawara ayi sulhu da su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel