Muna tattaunawa da Sin domin samun magungunan COVID-19 inji Onyeama

Muna tattaunawa da Sin domin samun magungunan COVID-19 inji Onyeama

- Najeriya ta na neman Sin ta taimaka mata da magungunan COVID-19

- Geoffery Onyeama ne ya bayyana haka bayan haduwa da Ministan Sin

- Gwamnatin Tarayya ta yaba da irin gudumuwar da kasar ta bada a da

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara magana da gwamnatin kasar Sin da nufin samun magungunan cutar nan ta COVID-19 ga mutanen Najeriya.

Ministan harkokin kasar wajen Najeriya, Geoffery Onyeama, ya bayyana wannan a lokacin da ya yi magana da manema labarai jiya a garin Abuja.

Hukumar dillacin labarai na kasa, NAN, ta ce Geoffery Onyeama ya zanta da ‘yan jarida ne bayan ya gana da takwaransa na kasar Sin, Wang Yi.

Mista Wang Yi ya kawo ziyarar aiki zuwa Najeriya domin ganin yadda Sin za ta taimakawa kasar.

KU KARANTA: COVID-19 ta harbi mutum 1300 a ranar Talata

Ministan harkokin kasar wajen ya bayyana cewa Sin ta taimakawa Najeriya matuka tun da aka fara fama da wannan annoba ta hanyar bada kayan aiki.

Onyeama ya ce a halin yanzu akwai kasashen da su ke kokarin gano maganin cutar, daga ciki har da kasar Sin, kuma Najeriya za ta nemi taimakonta.

“Muna samun gudumuwa sosai daga kasar Sin a bangaren bada kayan aikin likitoci na PPE, sun yi maza sun taimaka mana da kayan.” Inji Onyeama.

Ya ce: “Sin ta na cikin kasashen da ta gano maganin COVID-19, saboda haka muna magana da ita ta taimaka mana da magungunan saboda mutanenmu.”

KU KARANTA: ASUU ta ji shiru, ta fara yi wa Gwamnati barazanar tafiya wani sabon yajin-aiki

Muna tattaunawa da Sin domin samun magungunan COVID-19 inji Onyeama
Taron China-Nigeria Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Daily Trust ta rahoto Ministan yana bayanin niyyar Najeriya na ganin an rika samun jirgin sama wanda zai rika tashi kai tsaye daga Najeriya zuwa Sin.

Shugaban kwamitin PTF, Boss Mustapha ya bayyana cewa an yi wa masu NYSC fiye da 35, 000 gwajin COVID-19, kuma an gano 731 sun kamu da cuta.

PTF ta ce an samu masu hidimar kasa daga duka Jihohi 36 da ke dauke da COVID-19

Da yake jawabi a ranar Talata, Mista Boss Mustapha ya ce kwamitin PTF ya yi amfani da gwajin gaggawa na RDT a kan wadanda NYSC ta ke yi wa horo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel