Ba mu gamsu ba; magabatan Janar rundunar soji sun bayyana shakku a kan cewa korona ce ajalinsa

Ba mu gamsu ba; magabatan Janar rundunar soji sun bayyana shakku a kan cewa korona ce ajalinsa

- A makon jiya ne rundunar soji ta fitar da sanarwar cewa annobar Korona ta hallaka Janar Olubunmi Irefin sakamakon kamuwa da cutar

- Sai dai, ma su fada a ji daga yankin da marigayin ya fito sun ce sam basu gamsu cewa zai kamu da korona har ta hallaka shi duk cikin kwana uku kacal ba

Mutanen Aiyetoro-Gbede a jihar Kogi sun ƙi yarda da iƙirarin da hukumomin rundunar soji suka yi akan cewa dansu kuma amininsu, Marigayi Manjo Janar Olubunmi Irefin, ya rasu sanadiyyar kamuwa da cutar Korona(COVID-19).

Saboda haka, sun tsaya tsayin daka don binciko asalin dalilin mutuwarsa, kamar yadda Punch ta rawaito.

Jawabin ƙin amincewarsu da maganar rundunar soji ya zo ne cikin wata takarda mai sa hannun shugaban ƙungiyar cigaban Ayetoro-Gbede, Cif A. A Aminu, a ranar Asabar.

Sanata Dino Melaye, wanda ya fito daga garin, ya tabbatar da maganar ga ƴan jaridu yayin da aka tuntuɓe shi.

Cif Aminu ya ce ya bada jawabin ne a madadin Olu (Sarkin) Ayetoro Gbede, Oba D.S Ehindero, ƙungiyar cigaban Ayetoro, da kuma Majalisar masaurutun gargajiya.

KARANTA: Katsina: DHQ ta baza sojojin kasa da na sama neman daliban sakandiren Kankara

Rundunar Sojin Najeriya ce ta sanar da mutuwar Marigayi Janar Irefin a ranar 10 ga watan Disamba, 2020. Sanarwar ta ce ya rasu sanadiyyar kamuwa da kwayar cutar COVID-19.

Ba mu gamsu ba; magabatan Janar rundunar soji sun bayyana shakku a kan ce korona ce ajalinsa
Ba mu gamsu ba; magabatan Janar rundunar soji sun bayyana shakku a kan ce korona ce ajalinsa @Premiumtimes
Asali: Twitter

Sai dai, magabata da aminan marigayi Janar Irefin sun ce akwai lauje cikin naɗi kuma da walakin, wai goro a cikin miya, akwai bukatar duba irin wannan mutuwar bazata da ya yi.

Jawabin na su ya ce; "abubuwan da suka faru kafin mutuwar Janaral Irefin da kuma ainihin sanadiyyar rasuwarsu kamar yadda rundunar soji suka faɗi, sun haifar da shakku.

"Al-ummar Ayetola-Gbede, wanda suka haɗar da Majalisar Masaurata, da ƙungiyar cigaban Ayetola, sun ɗauki aniyar binciko ainihin sababin mutuwarsa.

"Kada mu manta cewa Janaral Olubunmi Irefin ya zo Ayetoro Gbede sati biyu da suka gabata don halartar jana'izar mahaifiyarsa."

KARANTA: Bidiyo: An daura auren Suleiman da Ba-Amurkiyya, Jenine, a Kano cikin annashuwa

"A wannan ɗan ƙanƙanin lokaci da ya zo, mun lura da cewa duk motsin sa akwai sojoji tattare da shi."

"Kwatsam, sai aka turo masa saƙo daga Abuja a kan cewa ya halarci wani taron tattaunawa tare da shugaban sojoji wanda ya fara daga 7 ga watan Disamba, 2020.

"Bamu samu labarin ya kamu da wata cuta ba, sai sanarwar da ta fito 10 ga watan Disamba, 2020, wai Janaral ya rasu sanadiyyar COVID-19, tare da kuma gaggawar binne shi da aka yi ranar Asabar, 12 ga watan Disamba, 2020.

"Idan lokacin bayyanar cutar Korona sati biyu ne, to alamu za su fara bayyana kamar zazzaɓi, ciwon kai, ya akayi irin wadannan alamun basu faru da Janaral Irefin ba?

"Shin waɗannan alamomin na sama suna kashe mutum ne nan take?"

"Duk da yawan shekarun tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, ya ɗauki makonni ya na fama da cutar, kafin ya rasu yana da shekaru 80,."

"A Tunani da hankali ya kamata ace a ƙaranchin shekarunsa idan har ya kamu da cutar, ya kamata ya ɗauki lokacin da yafi haka tsawo kafin rasuwarsa."

"Sai dai ko idan akwai wata COVID-19 ɗin da bamu sani ba, amma COVID-19 da muka sani bata kashe wanda ya kamu da ita cikin kwanaki uku."

"Me yasa hukumomin soji suka yi hanzarin binne shi?

"Har sai an bamu gamsassun amsoshi daga hukumomin soji dangane da waɗannan tambayoyi sannan za mu iya yarda da dalilin mutuwar tasa."

Legit.ng ta wallafa cewa sakamakon harin da yan bindiga suka kai makarantar, gwamna Aminu Bello Masari, ya bada umurnin kulle dukkan makarantun kwanan jihar Katsina.

Gwamnan ya bada umurnin ne yayin magana da manema labarai bayan ziyarar da ya kai makarantan ranar Asabar.

Masari ya ce a kulle makarantun kuma dalibai su koma gidajensu.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel