Eh, an nakasta shi; Kwamandan Boko Haram ya fadi gaskiyar halin da Shekau ke ciki

Eh, an nakasta shi; Kwamandan Boko Haram ya fadi gaskiyar halin da Shekau ke ciki

- An dade ana rade-radi tare da yada jita-jita a kan halin da shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ke ciki

- Wani matashin mayaki a kungiyar da aka kama ya fallasa gaskiyar halin da Shekau ke ciki a halin yanzu

- Matashin mayakin ya bayyana cewa ya zama mamba a kungiyar ne bayan mayakan kungiyar sun sace shi bayan sun kai hari garinsu

Wani mayakin kungiyar Boko Haram da aka kama ya bayyana cewa shugaban kungiyar, Abubakar Shekau, ya samu nakasa a kafafunsa, a saboda haka ba ya iya tafiya daidai, kamar yadda TheCable ta wallafa.

Matashin mayakin mai suna Mohammed Adam, wanda dakarun rundunar soji suka kama, ya ce Shekau ya samu raunuka a wani luguden wuta da sojoji suka yi a sansanin 'yan Boko Haram.

A cewarsa, lamarin ya faru ne a yankin Tumbuktu da ke cikin dajin Sambisa, babbar maboyar kungiyar Boko Haram a jihar Borno.

A wani faifan bidiyo da TheCable ta yi ikirarin cewa ta gani, Adam ya bayyana cewa yanzu Shekau ba zai iya jagorantar mayakansa zuwa wata fafatawa ko artabu ba.

KARANTA: Bidiyon Sheikh Karibu Kabara: Ina ajiye da zirin gashin Annabi da aka bani kyauta shekaru 8 da suka gabata

An dade ba'a ga Shekau a tsaye ya na magana a faifayen bidiyo da ya fitar a 'yan kwanakin baya bayan nan ba, kamar yadda ya saba yi a baya.

Eh, an nakasta shi; Kwamandan Boko Haram ya fadi gaskiyar halin da Shekau ke ciki
Eh, an nakasta shi; Kwamandan Boko Haram ya fadi gaskiyar halin da Shekau ke ciki @Thecable
Asali: Twitter

Adam ya zama mamba a kungiya Boko Haram tun ya na da shekaru goma bayan mayakan kungiyar sun tafi da shi lokacin da suka kai hari garinsu, Firgi, da ke yankin karamar hukumar Gwoza.

Matashin mayakin ya yi ikirarin cewa ya shafe tsawon shekaru biyar ya na fita yaki a tawagar da Shekau, da kansa, ke bawa umarni.

KARANTA: Bidiyon yadda Maina ya yanke jiki ya fadi a kotu

Ya bayyana cewa ya san Shekau sosai Kuma yana daga cikin mayakan da suka raka 'yammatan Chibok zuwa wurin da aka boyesu a sansanin 'yan Boko Haram da ke Tumbuktu.

A yayin da ya ke bawa rundunar soji tabbacin cewa ya yi yaki da mayakan kungiyar Boko Haram, Adam ya nuna irin dabarun sarrafa makamai da dasa sinadarai masu fashewa da ya koya a kungiyar.

"Na samu horo sosai a bangaren amfani da sarrafa makamai irinsu bindigar AK47, GPMG, da dasa bama-bamai a hanyoyin da sojoji ke bi," kamar yadda ya bayyana cikin yaren Hausa.

Adam ya ce an kai hare-hare masu yawa tare da shi kafin daga bisani ya sulale ya bar dajin Sambisa sakamakon ballewar annobar kwalera, amma sai ya fada hannun jami'an tsaro.

A ranar Juma'a ne Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa kotun ICC mai tuhumar manyan laifukan ta'addanci da cin zarafin jama'a ta ce za ta binciki hukumomin tsaron Nigeria.

Mai gurfanarwa a kotun ta ce ofshinta ya na kwararan hujjoji na zahiri da za'a iya kimantasu a kan jami'an hukumomin tsaron Nigeria.

Fatou Bensouda, mai gurfanarwa da ke shirin barin gado, ta lissafa wasu manyan laifuka da ICC ke zargin jami'an tsaron da aikatawa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel