Gwamnatin Tarayya ta amince a kashe N59.3bn a aikin titi da filin jirgin sama

Gwamnatin Tarayya ta amince a kashe N59.3bn a aikin titi da filin jirgin sama

- Gwamnatin Tarayya za ta gyara titin da ya hada Kaduna da Jihar Filato

- Za kuma ce ayi aikin hanyar Yakassai-Badume-Damargu-Makinzali a Kano

- Hadi Sirika ya ce Gwamnati za ta fadada filin jirgin sama na jihar Borno

A ranar Laraba, 9 ga watan Disamba, 2020, majalisar FEC ta amince da bukatar batar da N59.35 wajen gyaran hanyoyi da aikin filin jirgin sama.

Jaridar Vanguard ta ce Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya gabatar da takardun kwangila na aikin N50.858bn da yake so a duba.

A zaman da aka yi jiya, FEC ta yi na’am da wannan bukata na gyaran titi a jihar Kano kuma aikin hanyar Kano zuwa Filato wanda za scu ci N50bn.

Majalisar zartarwar kasar ta yarda a ba kamfanin CCECC aikin gina titin Yakassai-Badume-Damargu-Makinzali a jihar Kano a kan kudi N12.157bn.

KU KARANTA: Buhari ya soki CNN da BBC

Haka zalika kamfanin Setraco Nigeria Limited za su gyara hanyar Kaduna-Panbegua-Jos. Wannan katafaren aiki zai ci gwamnatin tarayya N38.701bn.

Shi ma Ministan birnin tarayya, Mallam Mohammed Bello, ya samu an amince da wasu tituna biyu da yake so ya yi a Abuja; Yaba-Kpahe da na Kwali/Abaji.

Rahoton ya nuna Ministocin sun kuma sake duba kudin da za a kashe wajen gyara titin Ring Road III zuwa Rind Road IV har zuwa Abuja industrial Park.

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, a madadin Ministan harkokin jirgin sama, Hadi Sirika, ya ce an yarda a fadada filin jirgi na Maiduguri.

Gwamnatin Tarayya ta amince a kashe N59.3bn a aikin titi da filin jirgin sama
Taron FEC
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya tayi maza ta karyata zargin da kasar Amurka take yi mata

Fadada filin sauka da tashin jirgin saman zai ci N719, 117, 868.60. Kamfanin Luvaslink Projects Limited za su yi aikin kamar yadda Lai Mohammed ya fada.

A jiya mun kawo maku jerin manya-manyan labaran da suka girgiza Najeriya a cikin shekarar 2020, daga ciki har da labaran #EndSARS, COVID-19,da sauransu.

Idan za ku tuna a shekarar nan ne Abba Kyari, Ismaila Funtua da Wada Maida su ka rasu. Dukkaninsu su na cikin manyan na kusa da shugaban Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel