Bukin Maulud: Muhimman abubuwa 5 da Buhari ya faɗa wa yan Nigeria

Bukin Maulud: Muhimman abubuwa 5 da Buhari ya faɗa wa yan Nigeria

- Yayinda Najeriya ke bikin haihuwar annabi Muhammadu a ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoba, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga yan Najeria kan wasu muhimman batutuwa

- Buhari ya ja hankalin al’umman kasar a cikin sakonsa na rana wannan rana ta Maulidi

- Sakon Shugaban kasar na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Garba Shehu, babban mai bashi shawara a kafofin watsa labarai

Legit.ng ta zakulo maku wasu muhimman batutuwa biyar da Shugaban kasar ya yi a sakon nasa.

KU KARANTA KUMA: Daga ƙarshe: Mazauna Legas sun roƙi ƴan sanda su koma bakin aiki

Bukin Maulud: Muhimman abubuwa 5 da Buhari ya faɗa wa yan Nigeria
Bukin Maulud: Muhimman abubuwa 5 da Buhari ya faɗa wa yan Nigeria Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

1. Ku nuna kauna da fahimta ga sauran yan uwanku ‘yan kasa

Shugaban kasar ya bukaci yan Najeriya da su amfani da wannan biki wajen koyi da kyawawan halayen annabi Muhammadu (SAW) ta hanyar nuna kauna da fahimta ga al'umman kasar.

Ya kuma bukaci su bayyanar da kyawawan halayensa na hakuri, gaskiya, rikon amana da mutunci ga kowa.

KU KARANTA KUMA: 2023: Kudu maso gabas ne ya kamata ya samar da magajin Buhari – Gwamna Umahi

2. Sako zuwa ga matasan Najeriya

Da yake misali da yawan rikice-rikice da sace-sace da aka fuskanta a fadin kasar bayan wasu bata gari sun janye zanga-zangar EndSARS, Shugaba Buhari ya bukaci matasan Najeriya da su “yi watsi da duk wasu munanan halayya.”

3. Za a hukunta wadanda suka yi sace-sace

Shugaba Buhari ya sha alwashin tabbatar da hukunta dukkanin wadanda ke da hannu a sace-sacen kayayyakin gwamnati da na mutane masu zaman kansu a fadin kasar.

4. Hukunta azzaluman jami’an yan sanda

Buhari ya kuma tabbatar da cika alkawarinsa na yin adalci ga duk wanda jami'in 'yan sanda suka zalinta.

5. Gargadi a kan annobar korona

Kan annobar korona, Shugaba Buhari ya bayyana cewa zuwa yanzu Najeriya ta yi nasarar magance matsalar ta hanyar tabbatar da adadin mutanen ya yi kasa.

Ya kuma shawarci duk 'yan Najeriya da su kiyaye dokokin kamuwa daga cutar COVID-19, kamar wanke hannaye, saka takunkumi da dokar nesa-nesa da juna.

A wani labarin, Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta amince da ware makudan kuɗaɗe domin horar da matasa dubu ɗari biyar 500,000 sabbin sana'o'i ta hanyoyin sarrafa fasahar zamani.

Ministan harkokin matasa da wasanni, Sunday Dare, ne ya bayyana hakan a wani taron matasa da kamfanin NBC (Nigeria Bottling Company) ya ɗauki nauyi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel